+ -

عَن عَلِيٍّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
أَخَذَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَرِيرًا بِشِمَالِهِ، وَذَهَبًا بِيَمِينِهِ، ثُمَّ رَفَعَ بِهِمَا يَدَيْهِ، فَقَالَ: «إِنَّ هَذَيْنِ حَرَامٌ عَلَى ذُكُورِ أُمَّتِي، حِلٌّ لِإِنَاثِهِمْ».

[صحيح] - [رواه أبو داود والنسائي وابن ماجه] - [سنن ابن ماجه: 3595]
المزيــد ...

Daga Aliyu ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe alhariri da hagunsa, kuma zinare da damansa, sannan ya ɗaga hannayensa da su, sai ya ce: "Lallai waɗannan biyun haramun ne ga mazan al'ummata, kuma halal ne ga matansu".

[Ingantacce ne] - - [سنن ابن ماجه - 3595]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe wani tufafi na alhariri ko wani yanki daga gare shi, da hannunsa na hagu, kuma ya riƙe zinariya ta ado ko mai kama da ita, da hannunsa na dama, sannan ya ce: Lallai alhariri da zinariya, sanya su haramun ne akan maza, amma mata to su halal ne garesu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Malayalam Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. AlSindi ya ce: (Haramun): Abin nufi yin anfani da su a sawa; inba haka ba ai yin anfani canji da ciyarwa da siyarwa ya halatta, yin anfani da zinariya ta hanyar sarrafata kwanuka da yin anfani da su to haramun ne.
  2. Yalwar shari'ar musulunci ga mata dan buƙata zuwa ga ado da makancinsa.