+ -

عَنِ الْمِقْدَادِ بْنِ الْأَسْوَدِ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ:
«تُدْنَى الشَّمْسُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنَ الْخَلْقِ، حَتَّى تَكُونَ مِنْهُمْ كَمِقْدَارِ مِيلٍ»، قَالَ سُلَيْمُ بْنُ عَامِرٍ: فَوَاللهِ مَا أَدْرِي مَا يَعْنِي بِالْمِيلِ؟ أَمَسَافَةَ الْأَرْضِ، أَمِ الْمِيلَ الَّذِي تُكْتَحَلُ بِهِ الْعَيْنُ قَالَ: «فَيَكُونُ النَّاسُ عَلَى قَدْرِ أَعْمَالِهِمْ فِي الْعَرَقِ، فَمِنْهُمْ مَنْ يَكُونُ إِلَى كَعْبَيْهِ، وَمِنْهُمْ مَنْ يَكُونُ إِلَى رُكْبَتَيْهِ، وَمِنْهُمْ مَنْ يَكُونُ إِلَى حَقْوَيْهِ، وَمِنْهُمْ مَنْ يُلْجِمُهُ الْعَرَقُ إِلْجَامًا» قَالَ: وَأَشَارَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِيَدِهِ إِلَى فِيهِ.

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2864]
المزيــد ...

Daga Miƙdad ɗan Aswad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
«Za'a kusantowa halitta da rana a yinin Alƙiyama har sai ta kusa kamar gwargwadan mil daga gare su», Sulaim ɗan Amir ya ce: Na rantse da Allah ban san me yake nufi da mil ba? Shin faɗin ƙasa ne, ko kuma mil ɗin da ake wa ido kwalli da shi? - ya ce: «Sai mutane su zama akan gwargwadan ayyukansu cikin gumi, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa idanun sawunsa, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa guwoyinsa, daga cikinsu akwai wanda zai kasance zuwa kwankwasonsa, daga cikinsu akwai wanda zai yi masa linzmi linzami» ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi nuni da hannunsa zuwa bakinsa.

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2864]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa za'a kusanto wa halitta rana a yinin alƙiyama, har ta zama kamar mil ne daga kawunansu. Tabi'i Sulaim ɗan Amir ya ce: Na rantse da Allah ban san waɗanne mil ɗin ake nufi ba, shin faɗin ƙasa, ko kuma mil ɗin da akewa ido kwalli da shi? Ya ce: Sai su zama akan gwargwadan ayyukansu a gumi; daga cikinsu akwai wanda guminsa zai kai zuwa idanun sawunsa, daga cikinsu akwai wanda zai kai zuwa gwiwowinsa, daga cikinsu wanda zai kai zuwa kwankwasonsa da maɗaurin tazugensa, daga cikinsu akwai wanda guminsa zai kai zuwa bakinsa sai ya hana shi magana. Ya ce: Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi nuni da hannunsa zuwa bakinsa.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin tshin hankalin ranar alƙiyama da kuma tsoratarwa daga garesu.
  2. Mutane zasu zama akan gwargwadan ayyukansu a cikin tsanani a ranar alƙiyama a farfajiyarta.
  3. Kwaɗaitarwa akan ayyukan alheri, da kuma tsoratarwa daga ayyukan sharri.