عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم قَالَ:
«دَعُونِي مَا تَرَكْتُكُمْ، إِنَّمَا هَلَكَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ بِسُؤَالِهِمْ وَاخْتِلَافِهِمْ عَلَى أَنْبِيَائِهِمْ، فَإِذَا نَهَيْتُكُمْ عَنْ شَيْءٍ فَاجْتَنِبُوهُ، وَإِذَا أَمَرْتُكُمْ بِأَمْرٍ فَأْتُوا مِنْهُ مَا اسْتَطَعْتُمْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 7288]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku barni a abinda na bar muku, kaɗai waɗanda ke gabaninku sun halaka ne da tambayarsu da kuma saɓawarsu ga annabawansu, idan na haneku daga wani abu to ku nuisance shi, idan na umarceku da wani abu to ku zo da shi daidai ikonku".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 7288]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ambaci cewa hukunce-hukuncen shari'a sun rabu gida uku: Abinda aka yi shiru akan sa, da abubuwan da aka hana, da abubuwan da aka yi umarni.
Amma na farko: Shi ne wanda shari'a ta yi shiru akansa, ta yadda babu wani hukunci, sai kuma cewa asali a abubuwa rashin wajabci; amma a zamaninsa - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - to barin tambaya ga wani abu da bai afku ba yana wajaba dan tsoron kada a wajabta ko haramci ya sauka a kan shi, domin Allah Ya bar su ne dan rahama ga bayi. Amma bayan rasuwarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan tambayar ta kasance ta fuskar neman fatawa ce ko koyarwa ga abinda ake buƙatuwa a gare shi na al'amarin addini to ya halatta, kai an yi umarni da shi ma, idan kuma ta fuskar ta'annututi ce da ɗorawa kai to shi ne abinda ake nufi da barin tambaya daga gare shi a cikin wannan Hadisin; hakan domin cewa shi zai iya kaiwa zuwa kwatankwacin abinda ya afku ga Banu Isra'ila, dan an umarce su su yanka saniya da sun yanka kowacce irin saniya da sun aikata umarni, sai dai su sun tsananta sai aka tsananta musu.
Na biyu: Abubuwan da aka hana; su ne: Abinda ake bawa wanda ya bar shi lada, kuma ana yi wa wanda ya aikata shi uƙuba, to nisantarsu yana wajaba.
Na uku: Abubuwan da aka umarta; shi ne abinda ake bawa wanda ya aikata shi lada, kuma ana yi wa wanda ya bar shi uƙuba, to yana wajaba ya aikata shi gwargwadan iko.