عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«خَيْرُ يَوْمٍ طَلَعَتْ عَلَيْهِ الشَّمْسُ يَوْمُ الْجُمُعَةِ، فِيهِ خُلِقَ آدَمُ، وَفِيهِ أُدْخِلَ الْجَنَّةَ، وَفِيهِ أُخْرِجَ مِنْهَا، وَلَا تَقُومُ السَّاعَةُ إِلَّا فِي يَوْمِ الْجُمُعَةِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 854]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a, a cikinsa ne aka halicci (Annabi) Adam, kuma a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, kuma a cikinsa ne aka fitar da shi daga gareta, kuma AlKiyama ba za ta tsayaba sai a ranar Juma'a".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 854]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafificin yinin da rana ta ɓullo a ciknsa shi ne yinin Juma'a. Daga abinda (ginin Juma’a) ya keɓa ta da shi: Allah Ya halicci (Annabi) Adam - aminci ya tabbata agare shi - a cikinsa, a cikinsa ne aka shigar da shi aljanna, a cikinsa ne aka fitar da shi daga aljannar, kuma aka sakko da shi ƙasa, Alkiyama ba za ta tashiba sai a yinin Juma'a.