عن أنسٍ رضي الله عنه قال: رَأَيْتُ رسولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم جَالِسًا مُقْعِيًا يَأْكُلُ تَمْرًا.  
                        
[صحيح] - [رواه مسلم]
                        
 المزيــد ... 
                    
Daga Anas, Allah ya yarda da shi, ya ce: Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana zaune a daure, yana cin dabino. 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi]                                            
Anas, Allah ya kara yarda a gare shi, ya ce: Na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana zaune tare da bayan sa a hade da kasa tare da kafafuwan sa a tsaye suna cin dabino. Don kada ya ci da yawa, to a wannan yanayin ba shi da kwanciyar rai, kuma ba zai ci da yawa ba.