+ -

عَنْ أَبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«مَا مِنْ صَاحِبِ ذَهَبٍ وَلَا فِضَّةٍ، لَا يُؤَدِّي مِنْهَا حَقَّهَا، إِلَّا إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ، صُفِّحَتْ لَهُ صَفَائِحُ مِنْ نَارٍ، فَأُحْمِيَ عَلَيْهَا فِي نَارِ جَهَنَّمَ، فَيُكْوَى بِهَا جَنْبُهُ وَجَبِينُهُ وَظَهْرُهُ، كُلَّمَا بَرَدَتْ أُعِيدَتْ لَهُ، فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ، حَتَّى يُقْضَى بَيْنَ الْعِبَادِ، فَيَرَى سَبِيلَهُ، إِمَّا إِلَى الْجَنَّةِ، وَإِمَّا إِلَى النَّارِ» قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، فَالْإِبِلُ؟ قَالَ: «وَلَا صَاحِبُ إِبِلٍ لَا يُؤَدِّي مِنْهَا حَقَّهَا، وَمِنْ حَقِّهَا حَلَبُهَا يَوْمَ وِرْدِهَا، إِلَّا إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ، بُطِحَ لَهَا بِقَاعٍ قَرْقَرٍ، أَوْفَرَ مَا كَانَتْ، لَا يَفْقِدُ مِنْهَا فَصِيلًا وَاحِدًا، تَطَؤُهُ بِأَخْفَافِهَا وَتَعَضُّهُ بِأَفْوَاهِهَا، كُلَّمَا مَرَّ عَلَيْهِ أُولَاهَا رُدَّ عَلَيْهِ أُخْرَاهَا، فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ، حَتَّى يُقْضَى بَيْنَ الْعِبَادِ، فَيَرَى سَبِيلَهُ إِمَّا إِلَى الْجَنَّةِ، وَإِمَّا إِلَى النَّارِ» قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، فَالْبَقَرُ وَالْغَنَمُ؟ قَالَ: «وَلَا صَاحِبُ بَقَرٍ، وَلَا غَنَمٍ، لَا يُؤَدِّي مِنْهَا حَقَّهَا، إِلَّا إِذَا كَانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ بُطِحَ لَهَا بِقَاعٍ قَرْقَرٍ، لَا يَفْقِدُ مِنْهَا شَيْئًا، لَيْسَ فِيهَا عَقْصَاءُ، وَلَا جَلْحَاءُ، وَلَا عَضْبَاءُ تَنْطَحُهُ بِقُرُونِهَا وَتَطَؤُهُ بِأَظْلَافِهَا، كُلَّمَا مَرَّ عَلَيْهِ أُولَاهَا رُدَّ عَلَيْهِ أُخْرَاهَا، فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ، حَتَّى يُقْضَى بَيْنَ الْعِبَادِ، فَيَرَى سَبِيلَهُ إِمَّا إِلَى الْجَنَّةِ، وَإِمَّا إِلَى النَّارِ» قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، فَالْخَيْلُ؟ قَالَ: «الْخَيْلُ ثَلَاثَةٌ: هِيَ لِرَجُلٍ وِزْرٌ، وَهِيَ لِرَجُلٍ سِتْرٌ، وَهِيَ لِرَجُلٍ أَجْرٌ، فَأَمَّا الَّتِي هِيَ لَهُ وِزْرٌ، فَرَجُلٌ رَبَطَهَا رِيَاءً وَفَخْرًا وَنِوَاءً عَلَى أَهْلِ الْإِسْلَامِ، فَهِيَ لَهُ وِزْرٌ، وَأَمَّا الَّتِي هِيَ لَهُ سِتْرٌ، فَرَجُلٌ رَبَطَهَا فِي سَبِيلِ اللهِ، ثُمَّ لَمْ يَنْسَ حَقَّ اللهِ فِي ظُهُورِهَا وَلَا رِقَابِهَا، فَهِيَ لَهُ سِتْرٌ وَأَمَّا الَّتِي هِيَ لَهُ أَجْرٌ، فَرَجُلٌ رَبَطَهَا فِي سَبِيلِ اللهِ لِأَهْلِ الْإِسْلَامِ، فِي مَرْجٍ وَرَوْضَةٍ، فَمَا أَكَلَتْ مِنْ ذَلِكَ الْمَرْجِ، أَوِ الرَّوْضَةِ مِنْ شَيْءٍ، إِلَّا كُتِبَ لَهُ، عَدَدَ مَا أَكَلَتْ حَسَنَاتٌ، وَكُتِبَ لَهُ، عَدَدَ أَرْوَاثِهَا وَأَبْوَالِهَا، حَسَنَاتٌ، وَلَا تَقْطَعُ طِوَلَهَا فَاسْتَنَّتْ شَرَفًا، أَوْ شَرَفَيْنِ، إِلَّا كَتَبَ اللهُ لَهُ عَدَدَ آثَارِهَا وَأَرْوَاثِهَا حَسَنَاتٍ، وَلَا مَرَّ بِهَا صَاحِبُهَا عَلَى نَهْرٍ، فَشَرِبَتْ مِنْهُ وَلَا يُرِيدُ أَنْ يَسْقِيَهَا، إِلَّا كَتَبَ اللهُ لَهُ، عَدَدَ مَا شَرِبَتْ، حَسَنَاتٍ» قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ، فَالْحُمُرُ؟ قَالَ: «مَا أُنْزِلَ عَلَيَّ فِي الْحُمُرِ شَيْءٌ، إِلَّا هَذِهِ الْآيَةَ الْفَاذَّةُ الْجَامِعَةُ»: {فَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ، وَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ} [الزلزلة: 8].

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 987]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta, sai a ƙona shi a kansu a cikin wutar Jahannama, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas, duk lokacin da suka ƙone sai a dawo da su, a cikin wani yinin da gawargwadansa shekara dubu hamsin ne, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai yaga hanyarsa, ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 987]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana nau'ika na dukiya, da sakamakon wanda bai bada zakkarsu ba a ranar alƙiyama, daga cikinsu:
Na farko: Zinare da azirfa da abinda ke cikin hukuncinsu na dukiyoyi da hajoji na kasuwanci, shi ne abinda zakka ta wajaba a cikinsa bai bayar ba, idan ranar alƙiyama ta zo za'a narka su aƙerasu akan siffar alluna, kuma a kunna wutar Jahannama a kansu, a yi masa azaba da su, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas da su, duk lokacin da suka yi sanyi sai a dawo da ƙunarsu, zai kasance a wannan halin na azaba tsawon ranar alkiyama wanda gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta.
Na biyu: Wanda ya mallaki raƙuman da ba ya bada farillar zakkarsu da kuma haƙƙinsu, daga ciki (akwai) tatsar nonansu ga wanda ya zo nema cikin miskinai, za’a zo da waɗannan raƙuman masu girma masu ƙiba kuma mafi yawa kan yadda suke a cikin adadinsu, za'a shinfiɗa shi a jefa shi a miƙar da mai su ranar alƙiyama akan wata ƙasa mai yalwa miƙaƙƙiya, zasu dinga takashi da ƙafafunsu, kuma zasu dinga cizonsa da haƙoransu, duk lokacin da na ƙarshensu ya wuce akansa za'a dawo da na farkonsu a kansa, zai zarce akan wannan halin na azaba tsawon yinin alƙiyama wace gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta.
Na uku: Wanda ya mallaki shanu da tumakai - wadanda suke tunkiyoyi da awakai - waɗanda mai su ba ya bada zakkarsu ta wajibi, za’a zo da su mafi yawan abinda da suke akai na adadi ba za’a tauye komai ba daga garesu, sai a shinfiɗasu a jefa shi kuma a miƙar da mai su a ranar lahira akan ƙasa mai yalwa madaidaiciya, babu wasu masu lanƙwasasshen ƙaho, ko waɗanda ba su da ƙahon, ko masu karyayyen ƙaho, kai su akan mafi cikar siffofinsu ne, sai su soke shi da ƙahonhunansu, kuma su taka shi da ƙafafuwansu, duk lokacin na ƙarshensu ya wuce a kan shi sai a dawo da na farkonsu. Zai ci gaba akan wannan halin na azaba tsawon yinin alƙiyama wacce gwargwadan yininta shekara dubu hamsin ne, har sai Allah Ya yi hukunci tsakanin halitta, sai ya zama daga 'yan aljanna ko daga 'yan wuta.
Na huɗu: Wanda ya mallaki dawakai, su dawakai nau'i uku ne:
Na farko: Su laifi ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan riya da alfahari da kuma yaƙar ma'abota Musulunci.
Na biyu: Su sutura ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan yin yaƙi a tafarkin Allah, sannan ya kyautata musu da ciyar da su da ragowar ɗawainiyarsu, daga cikinsu (akwai) barbarar namijinsu.
Na uku: Su lada ne gare shi, shi ne wanda ya riƙesu dan yin yaƙi a tafarkin Allah ga ma'abota Musulunci, su a cikin ciyayinsu da dausayinsu dan yin kiwo, to ba abinda zasu ci sai an rubuta masa kyakkyawa adadin abinda suka ci, kuma an rubuta masa kyakkyawa adadin torosonsu da fitsarinsu, ba'a yanke igiyarsu ba, ita ce igiyar da ake ɗauresu a cikinta, suka yi gudu kuma suka yi sukuwa a ƙasa maɗaukakiya; sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa adadin gurabensu da torosonsu, kuma ma'abocinsu bai wuce ba akan wata ƙorama sai su sha daga gareta kuma ba ya nufin ya shayar da su, sai Allah Ya rubuta masa kyakkyawa adadin abinda suka sha .
Sannan aka tambayi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi game da jakuna shin su irin dawakai ne?
Sai ya ce: Shar'antawa bai sauka ba a sha'aninsu sai dai wannan ayar wacce irinta kadan ne, ita mai gamewa ce ga dukkan nau'ikan ɗa'a da saɓo; ita ce faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Wanda ya aikata kwatankwacin ƙwayar komayya na alheri zai gan shi, wanda yaaikata kwatankwacin ƙwayar komayya na sharri zai ganshi}. [al-Zilzalah: 8], wanda ya yi aiki a cikin mallakar jakai dan yin ɗa'a zai ga ladan hakan, idan kuma ya aikata saɓo to zai ga uƙubar hakan, kuma wannan mai ƙunsar dukkan ayyuka ne.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الرومانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajabcin bada zakka, da narko mai tsanani akan hanata.
  2. Rashin kafircin wanda ya hana zakka dan kasala, sai dai cewa shi yana kan haɗari mai tsanani.
  3. Mutum ana ba shi lada akan rabe-raben da suke afkuwa a cikin aikata ɗa'a, idan ya nufi asalinta, koda bai yi nufin waɗancan rabe-raben ba.
  4. Akwai wani haƙƙi a cikin dukiya banda zakka.
  5. Daga haƙƙi a raƙuma (akwai) tatsar nononsu ga wanda ya zo wurinsu cikin miskinai a wurin da zasu sha ruwa; dan ya zama mafi sauƙi ga mabuƙaci daga nufin masaukai, kuma mafi sauƙi ga dabbobin, Ibnu Baɗɗal ya ce: A kwai haƙƙoƙi biyu a cikin dukiya: Farilla ta aini da waninsa, tatsar nonon yana daga haƙƙoƙin da suke daga cikin manyan ɗabi'u.
  6. Daga haƙƙi na wajibi a cikin raƙuma da shanu da tumakai barbarar namijinsu idan an nemi bada aronsa.
  7. Hukuncin jakai da dukkan abinda nassi bai zo da shi ba: Cewa shi mai shiga ne cikin faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Wanda ya aikata kwatankwacin ƙwayar komayya na alheri zai gan shi, wanda ya aikata kwatankwacin ƙwayar komayya na sharri zai gan shi}.
  8. A cikin ayar akwai kwaɗaitarwa a aikata aikin alheri koda kaɗan ne, da tsoratarwa daga aikata sharri ko da ƙasƙantacce ne.