Karkasawa: Falaloli da Ladabai .

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لاَ تَتَّخِذُوا الضَّيْعَةَ فَتَرْغَبُوا فِي الدُّنْيَا».

[حسن لغيره] - [رواه الترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 2328]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada ku riƙi gona sai ku yi kwaɗayin duniya".

[Hasan ne da wani Sanadin] - [Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi] - [Sunan Tirmizi - 2328]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga riƙon gona; domin hakan yana daga sabubban kwaɗayi a duniya da karkata zuwa gareta abar lahira.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani akan yawaita neman duniya da abinda yake kaiwa zuwa juyawa lahira baya.
  2. A cikin hadisin babu hani daga riƙon binda yake akwai abin samun rayuwa daga gare shi, kaɗai hani ne daga dulmiya a cikin duniya da kuma mantawa da lahira.
  3. Sindi ya ce: Abin nufi: Kada ku zirfafa a cikin riƙon gona sai ku shagalta da ita daga ambatan Allah.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (36)