عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما : «أنه كان يسير على جمل فأعيا، فأراد أن يُسَيِّبَهُ. فلحقني النبي صلى الله عليه وسلم فدعا لي، وضربه، فسار سيرا لم يَسِرْ مثله. ثم قال: بِعْنِيهِ بأُوقية. قلتُ: لا. ثم قال: بِعْنِيه. فَبِعْتُهُ بأوقية، واستثنيت حُمْلَانَهُ إلى أهلي. فلما بلغت: أتيته بالجمل. فنقدني ثمنه. ثم رجعت. فأرسل في إثري. فقال: أتَرَانِي مَاكستُكَ لآخذ جملك؟ خذ جملك ودراهمك، فهو لك».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Jabir Dan Abdullahi cewa shi ya kasance yana tafiya akan wani Rakuminsa da ya kasa tafiya, sai Annabi ya so ya hutar da shi, sai Annabi ya riskeni, sai ya yi mun Addua, kuma ya dake shi, sai ya zama ya ware yana tafiya ma tafiyar da bai taba yinta ba, sannan ya ce: ka siyarmun shi da Ukiya, amma saoi nace to banda kayansa har sai na isa gida, to yayin da na isa: sai na zo masa da Rakumin, sai ya bani kudina hannu, sannan na dawo, sai ya aiko bayana sai ya ce mun: "ko kana ganin na yi ta yi maka tayi don in kwace maka Rakuminka? Karbi Rakuminka da kudinka, na barmaka shi'
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Jabir ya kasance tare da Annabi a daya daga cikin yakunansa, kuma ya kaance yana kan Rakumi wanda ya rame, sai ya kaa tafiya da iya daidaita tafiyarsa da ayari, har cewa shi yaso ya kyale shi yai tafiyarsa shi kadai, sabida rashin amfaninsa kuma Annabi ya kasance sabida tausayinsa sa da Sahabbansa da kuma Al'ummasa yana tafiya ne a bayan Runduna don tausayawa rarrauna, da wanda ya gajiya da kuma wanda guzurinsa ya kare, sai ya gamu da Jabir yana kan Rakuminsa, sai yayi masa Addua kuma ya daki Rakumin, sai dukan mai girma ya zama jin kai da kuma karin karfi da taimako ga gajiyayyen Rakumi, sai ya fara tafiya tafiyar da bai taba yinta ba, sai Annabi sabida Karamcinsa da kyawawn Dabi'unsa da tausayawarsa ya so faranta ran Jabir da kuma daukarsa da Magana da zata dauke masa kewar tafiya, sai ya ce: to siyar mun da Rakumin da kimar Ukiyya to Jabir sai yai kwadayin falalar Allah kuma ya sani cewa babu tawaya a Adininsa da zai ki siyarwa Annabi Rakuminsa, domin wannan baya cikin biyayya ta wajibi, domin Umarnin bai zama na dole ba, kuma duk da haka Annabi ya kara tambayarsa da ya siyar masa da Ukiyya, kuma ya shardanta masa cewa zai ci gaba da hawa har zuwa gida Madina, ai Annabi ya yarda da sharadinsa da suka iso, sai ya zo masa da Rakumi, kuma ya bashi kudin yayin da ya koma sai ya aiko bayansa a kirawo shi kuma ya ce da shi, kana ganin na sayi Rakuminka don kwadayin in rabaka da shi? Dauki Rakuminka da kudinka duka na baka, kuma irin wannan ba abin Mamaki bane kan Karamcin Annabi da kuma halayyarsa da kuma tausasawarsa, kuma Annabi yana da irin wadan nan misalan manya a tarihinsa

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin