عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلَّى الله عليه وسلم قال:
«ما مِنْ أحَدٍ يُسلِّمُ علي إلا ردَّ اللهُ عليَّ رُوحي حتى أردَّ عليه السَّلامَ».
[إسناده حسن] - [رواه أبو داود وأحمد] - [سنن أبي داود: 2041]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Babu wani mutum da zai yi mini sallama har sai Allah Ya dawo mini da raina har sai na mayar masa da sallamar".
[Sanadi nsa Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 2041]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa shi ana dawo masa da ransa dan ya amsa sallama ga dukkan wanda ya yi masa sallama , daidai ne ya kasance a kusa yake ko a nesa; rayuwar barzahu da ƙabarbura wani al'amari ne na gaibu, babu wanda ya san haƙiƙaninsu sai Allah, Shi Mai iko ne akan dukkan komai.