عَنِ الأَسْوَدِ بنِ يَزِيدَ قَالَ:
سَأَلْتُ عَائِشَةَ مَا كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَصْنَعُ فِي بَيْتِهِ؟ قَالَتْ: كَانَ يَكُونُ فِي مِهْنَةِ أَهْلِهِ -تَعْنِي خِدْمَةَ أَهْلِهِ-، فَإِذَا حَضَرَتِ الصَّلاَةُ خَرَجَ إِلَى الصَّلاَةِ.
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 676]
المزيــد ...
Daga al-Aswad Ibnu Yazid ya ce:
Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 676]
An tambayi Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - game da halin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin gidansa kuma me yake aikatawa? Sai ta ce: Ya kasance mutum ne daga cikin mutane, yana aikata abinda maza suke aikatawa a cikin gidajensu, sai ya kasance a cikin hidimar kansa da iyalansa; yana tatsar nonon akuyarsa, yana ɗinke tufafinsa, yana gyara takalminsa, yana ɗinke gugansa, kuma ya kasance idan lokacin tada sallah ya yi sai ya fita zuwa gareta - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba tare da wani jinkiri ba.