kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mata daga matan Madina, dan mu yi masa caffa, sai muka ce: Ya manzon Allah, zamu yi maka caffa akan kada mu hada Allah da wani abu (a bauta), kada mu yi sata ba, kada mu yi zina, kada mu zo da ƙirƙirarriyar ƙarya da zamu aikata a tsakanin hannayenmu da ƙafafuwanmu, kuma kada mu saɓa maka a wani aikin alheri, ya ce: "A abinda zaku iya da abinda zaku samu ikon yi". Ta ce: Muka ce: Allah da manzonSa ne mafi tausayi garemu, zo mu yi maka caffa ya manzon Allah, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: @"Lallai ni bana gaisawa da mata, kawai maganata ga mata dari kamar maganata ce ga mace daya*, ko kwatankwacin magana ga mace ɗaya".
عربي Turanci Indonisiyanci
Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: @Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.
عربي Turanci urdu