+ -

عَنْ أُمَيْمَةَ بِنْتِ رُقَيْقَةَ رضي الله عنها أَنَّهَا قَالَتْ:
أَتَيْتُ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي نِسْوَةٍ مِنَ الْأَنْصَارِ نُبَايِعُهُ، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، نُبَايِعُكَ عَلَى أَلَّا نُشْرِكَ بِاللَّهِ شَيْئًا، وَلَا نَسْرِقَ، وَلَا نَزْنِيَ، وَلَا نَأْتِيَ بِبُهْتَانٍ نَفْتَرِيهِ بَيْنَ أَيْدِينَا وَأَرْجُلِنَا، وَلَا نَعْصِيَكَ فِي مَعْرُوفٍ، قَالَ: «فِيمَا اسْتَطَعْتُنَّ، وَأَطَقْتُنَّ» قَالَتْ: قُلْنَا اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَرْحَمُ بِنَا، هَلُمَّ نُبَايِعْكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي لَا أُصَافِحُ النِّسَاءَ، إِنَّمَا قَوْلِي لِمِائَةِ امْرَأَةٍ كَقَوْلِي لِامْرَأَةٍ وَاحِدَةٍ، أَوْ مِثْلُ قَوْلِي لِامْرَأَةٍ وَاحِدَةٍ».

[صحيح] - [رواه الترمذي والنسائي وابن ماجه] - [سنن النسائي: 4181]
المزيــد ...

Daga Umaimah 'yar Ruƙaiƙah - Allah Ya yarda da ita - cewa ita ta ce:
Na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mata daga matan Madina, dan mu yi masa caffa, sai muka ce: Ya manzon Allah, zamu yi maka caffa akan kada mu hada Allah da wani abu (a bauta), kada mu yi sata ba, kada mu yi zina, kada mu zo da ƙirƙirarriyar ƙarya da zamu aikata a tsakanin hannayenmu da ƙafafuwanmu, kuma kada mu saɓa maka a wani aikin alheri, ya ce: "A abinda zaku iya da abinda zaku samu ikon yi". Ta ce: Muka ce: Allah da manzonSa ne mafi tausayi garemu, zo mu yi maka caffa ya manzon Allah, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai ni bana gaisawa da mata, kawai maganata ga mata dari kamar maganata ce ga mace daya, ko kwatankwacin magana ga mace ɗaya".

[Ingantacce ne] - - [سنن النسائي - 4181]

Bayani

Umaimah 'yar Ruƙaiƙah - Allah Ya yarda da ita -: Cewa ita ta zo wurin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tare da ita akwai wasu mata daga matan Madina, zasu yi masa caffa (mubaya’a) akan ba zasu yi wa Allah shirka da wani abu ba, kuma ba zasu yi sata ba, ba zasu yi zina ba, ba zasu zo wa ƙirƙirarriyar ƙaryar ba da zasu aika tsakanin hannayensu da ƙafafuwansu ba, kuma ba zasu saɓa masa a wani aikin alheri ba, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: A cikin abinda zaku iya, kuma kuke da iko, Muka ce: Allah da manzonSa ne mafi jin ƙai da mu, ka zo mu yi maka caffa (mubaya’a) ya manzon Allah da gaisawa hannu da hannu kamar yadda maza suke yi maka, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Lallai ni bana gaisawa da mata hannu da hannu, kawai maganata da mubaya'ata ga mata ɗari kamar maganata ce ga mace ɗaya.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin yadda mubaya'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga mata take.
  2. Haramcin gaisawa da mata hannu da hannu banda muharramai.
  3. Hukunci na shari'a an rataya shi ne da iko da kuma yi yadda za'a iya.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin