+ -

عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
بَعَثَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَرِيَّةً فَاسْتَعْمَلَ رَجُلًا مِنَ الأَنْصَارِ، وَأَمَرَهُمْ أَنْ يُطِيعُوهُ، فَغَضِبَ، فَقَالَ: أَلَيْسَ أَمَرَكُمُ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنْ تُطِيعُونِي؟ قَالُوا: بَلَى، قَالَ: فَاجْمَعُوا لِي حَطَبًا، فَجَمَعُوا، فَقَالَ: أَوْقِدُوا نَارًا، فَأَوْقَدُوهَا، فَقَالَ: ادْخُلُوهَا، فَهَمُّوا، وَجَعَلَ بَعْضُهُمْ يُمْسِكُ بَعْضًا، وَيَقُولُونَ: فَرَرْنَا إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنَ النَّارِ، فَمَا زَالُوا حَتَّى خَمَدَتِ النَّارُ، فَسَكَنَ غَضَبُهُ، فَبَلَغَ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «لَوْ دَخَلُوهَا مَا خَرَجُوا مِنْهَا إِلَى يَوْمِ القِيَامَةِ؛ الطَّاعَةُ فِي المَعْرُوفِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4340]
المزيــد ...

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki wata ƙaramar runduna sai ya shugabantar da wani mutum daga cikin mutanen Madina, kuma ya umarcesu da su yi masa biyayya, sai (mutumin) ya yi fushi, sai ya ce: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai umarce ku ku bini ba? suka ce: Ya umarcemu. (Sai) Ya ce: Ku haɗa mini itatuwa, sai suka haɗa masa, sai ya ce: Ku kunna wuta, sai suka kunnata, sai ya ce: Ku shigeta, sai suka yi niyyar (shiga), sai wasu daga cikinsu suka riƙe wasu, suna cewa: Mun gujewa wuta ne zuwa wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, basu gushe ba har sai da wutar ta mutu, sai fushinsa ya gushe, sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: «Da a ce sun shigeta da ba zasu fita daga cikinta ba har zuwa ranar alƙiyama; biyayya tana kasancewa ne kawai a aikin alheri».

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4340]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki wata runduna, sai ya sanya wani mutum daga cikin mutanen Madina shugaba a kansu, kuma ya umarcesu da su yi masa biyayya, sai shugaban ya yi fushi a kansu kuma ya ce musu: Shin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai umarceku ku bini ba? Suka ce: Ya yi umarni, ya ce: To na umarceku ku tattara mini itace ku kunna wuta, sannan ku shiga cikinta, sai suka tara itatuwa suka kunna wuta, lokacin da suka yi yunkurin shiga cikinta, sai sashinsu ya fara kallon sashi. Suka ce: Lallai mu bamu bi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba sai donin gujewa wuta shin ma shigeta kuwa? Suna cikin haka sai wutar ta mutu, kuma fushin shugaba ya tafi. Sai aka baiwa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin hakan, sai ya ce: Da sun bi shi sun shiga cikin wutar da suka kunnata da an yi musu azaba a cikinta har ƙarewar duniya, babu biyayya ga wani abin halitta a cikin saɓon Mahalicci; kaɗai biyayya tana wajaba ne a aikin alheri ba'a saɓo ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin cewa ɗa'a (biyayya) kaɗai tana kasancewa ne a aikin alheri ba'a saɓo ba, koda wanda ya yi umarnin ya kasance daga cikin wanda ya wajaba a yi masa biyayya ne.
  2. Mai saɓo mai tauhidi an yi masa alkawarin narko da wuta, amma Allah zai iya gafarta masa.
  3. Halaccin sanya shugaba a cikin yaƙi, haka nan a halin tafiya.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami الهولندية الغوجاراتية الدرية المجرية الجورجية المقدونية
Manufofin Fassarorin