+ -

عن سهل بن سعد الساعدي رضي الله عنه مرفوعاً: "لأعطين الراية غدا رجلا يحب الله ورسوله ويحبه الله ورسوله، يفتح الله على يديه، فبات الناس يدوكون ليلتهم أيهم يعطاها فلما أصبحوا غدوا على رسول الله صلى الله عليه وسلم كلهم يرجو أن يعطاها: فقال: أين علي بن أبي طالب؟ فقيل: هو يشتكي عينيه، فأرسلوا إليه فأتي به، فبصق في عينيه، ودعا له فبرأ كأن لم يكن به وجع، فأعطاه الراية فقال: انفذ على رسلك حتى تنزل بساحتهم، ثم ادعهم إلى الإسلام وأخبرهم بما يجب عليهم من حق الله تعالى فيه، فوالله لأن يهدي الله بك رجلا واحدا خير لك من حمر النعم".
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce a ranar Khaibara:
"Lallai zan bai wa wani mutum wannan tutar Allah Zai yi buɗi ta hannunsa, yana son Allah da manzaonSa kuma Allah da manzonSa suna son shi". Ya ce: Sai mutane suka kwana suna tattaunawa a daran waye a cikinsu za'a ba shi ita, lokacin da mutane suka wayi gari sai suka yi jijjifi ga manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowanne su yana ƙaunar a ba shi ita, sai ya ce: "Ina Aliyu ɗan Abi Dalib?" sai aka ce : Shi ya manzon Allah yana ciwon idanu, ya ce: "Ku aike masa", sai aka zo da shi sai manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tofi a cikin (idanuwa) ya yi masa addu'a, sai ya warke kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, sai (Sayyidina) Aliyu ya ce: Ya manzon Allah, shin zan yake su ne har sai sun zama irinmu? sai ya ce: "Ka zarce a hankali har sai ka sauka a farfajiyarsu, sannan ka kira su zuwa ga musulunci, ka ba su labari da abinda yake wajaba akansu na hakkin Allah a cikinsa, na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen ni'imomi (rakuma)".

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya bai wa sahabbai labari da samun nasarar musulmai akan Yahudawan Khaibara a wayewar gari, hakan ta hannun wani mutum da zai ba shi tuta ne alamar da runduna take rikewa alama a gare ta. Wannan mutumin daga siffofinsa cewa shi yana son Allah da manzonSa, kuma Allah da manzonSa suna sonsa. Sai sahabbai suka kwana suna tunani suna tattaunawa ga wanda za'a bai wa tutar? dan kwaɗayin wannan matsayi mai girma, Lokacin da gari ya waye sai suka tafi zuwa wurin manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - kowannensu yana kwaɗayin ya rabauta da wannan matsayin,
sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi tambaya game da Aliyu ɗan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -?
sai aka ce : Lallai ba shi da lafiya, yana fama da ciwon idanunsa.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya aika a zo masa da shi, sai ya yi tofi a idon (sayyidina) Aliyu daga yawansu mai daraja, kuma ya yi masa Addu’a, sai ya warke daga cutar kai kace babu wani ciwo a tare da shi, sai ya ba shi tuta, kuma ya umarce shi da zarcewa cikin sauƙi har sai ya yi kusa daga ganuwar maƙiya sai ya bijiro musu da shiga musulunci, idan sun amsa masa; sai ya ba su labari da abinda yake wajaba akansu na farillai.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyanawa Aliyu falalar kira zuwa ga Allah, kuma mai Da'awah idan ya zama sababi a cikin shiriyar wani mutum ɗaya to hakan shi ne mafi alheri a gare shi da ya samu jajayen raƙuman da su ne mafi tsadar dukiyoyin Larabawa, sai ya mallakesu ko ya yi sadaka da su.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami السويدية الأمهرية القيرقيزية اليوروبا الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar (Sayyidina) Aliyu ɗan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi -, da shaidar manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - gare shi, da son Allah da manzonSa gare shi, da kuma soyayyarsa ga Allah da manzonSa.
  2. Kwaɗayin sahabbai akan alheri da rige-rigen su gare shi.
  3. Halaccin ladabi a gurin yaƙi da barin ɗimuwa da daga murya masu tsoratarwa waɗanda babu buƙatuwa zuwa gare su.
  4. Daga dalilan annabtar - tsira daa mincin Allah su tabbata agare shi - bada labarinsa da samun nasara akan Yahudawa, da warkar da idanuwan Aliyu ɗan Abi Dalib a hannunsa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da izinin Allah.
  5. Cewa manufa mafi girma a yaƙI ita ce shigar mutane cikin musulunci.
  6. Da'awa tana kasancewa da bi asannu-sannu sai a nema daga kafiri a farko ya shiga cikin muslunci ta hanyar furta kalmar shahada biyu, sannan a umarce shi da farillan musulunci bayan hakan.
  7. Falalar Da’awah zuwa musulunci da abinda ke cikinta na alheri ga wanda aka kira da mai kiran, wanda aka kira zai iya shiriya, mai kiran kuma za’a ba shi lada mai girma.