عن سعيد بن المسيب عن أبيه المسيب بن حزن رضي الله عنه قال: "لما حضرَتْ أبا طالب الوفاة جاءه رسول الله صلى الله عليه وسلم وعنده عبد الله بن أبي أمية وأبو جهل، فقال له: يا عَمِّ قل لا إله إلا الله، كلمة أُحَاجُّ لك بها عند الله، فقالا له: أَتَرَغَبُ عن ملة عبد المطلب؟ فأعاد عليه النبي صلى الله عليه وسلم ، فأعادا، فكان آخر ما قال هو على ملة عبد المطلب، وأبى أن يقول لا إله إلا الله، فقال النبي صلى الله عليه وسلم : لأستغفرن لك ما لم أُنْهَ عنك، فأنزل الله: {مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَنْ يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قربى...} الآية"، وأنزل الله في أبي طالب: {إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللَّهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ}.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

An karbo daga Sa'id Dan Almusayyib daga Babansa Almusayyib Dan Hazan Allah ya yarda dashi yace: "Yayinda Mutuwa tazowa Aba Dalib sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yazo masa atare dashi akwai Abdullah Dan Abi Umayya da Abu Jahal,sai yace dashi:Ya Baffana kace babu abin Bautawa da Gaskiya sai Allah;kalmace da zan maka dalili da ita awajan Allah.sai sukace dashi:ka ki kuwa Tafarkin Abdul Muddalib?sai Annabi tsira da aminci su tabbata agareshi ya kuma maimaita masa,sai suma suka kara maimaita masa.sai ya zama karshen abinda ya fada shi yana tafarkin Abdul Muddalib,yaki yace babu abin bautawa da Gaskiya sai Allah.sai Annabi tsira da aminci su tabbata agareshi yace:lallai sai na nema maka Gafara mutukar ba'a haneni ba.sai Allah ya saukar da:{bai kasance ga Annabi da wadanda suka bada Gaskiya su nemawa Mushirikai Gafara koda kuwa sun kasance Makusanta...}. sai Allah ya saukar akan Abi Dalib:{Hakika kai baka shiryar da wanda kaso sai dai Allah ne mai shiryar da wanda yaso kuma shine mafi sanin shiryayyu}.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi yaje gaida Abu Talib kuma yana halin Mutuwa kuma ya gabatar Masa da Musulunci; don rayuwarsa don ya samu rabauta Duniya da Lahira, kuma ya nemi ya furta kalmar Tauhidi, kuma Mushirikai suka gabatar masa akan cewa ya zauna kan Addinin Iyayensa shi ne shirka; sabida saninsu da abinda take nunawa na kore shirka da kuma tsarkake Ibada ga Allah shi kadai, kuma Annabi ya maimaita masa abinda ya nema na furta kalmar Shahada daga Baffansa, kuma Mushirikai suka kara futo na futo da shi kuma suka zamanto dalili na toshe shi daga gaskiya da kuma mutuwarsa akan shirka kuma wannan ya faru bayan Annabi don ya nema masa gafara matukar ba'a hana shi ba, sai Allah ya hana hakan kuma ya bayyana cewa hakan shiriya a hannun Allah da yake yin falalarsa ga wanda ya so; cewa shi yasan wanda ya cancanci wanda ya dace da haka, sai Allah ya saukar: {Bai dace da Annabi kuma da wanda sukai Imani ba su nemawa Mushrikai Gafara, kuma ko sun kasance makusantansu {ne bayanya bayyana cewa su yan Wuta ne kuma Allah ya saukar da ita ne kan Abu Talib: "Lallai kai cewa kai ba zaka iya shiryar da wanda ka so ba kuma Allah shi ne yake shiryar da wanda ya so, kuma Allah shi ne mafi sani da shiryayyu"

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin