عن أَبِي أُمَامَةَ إِياسِ بنِ ثَعْلَبَةَ الحَارِثِيِّ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«مَنِ اقْتَطَعَ حَقَّ امْرِئٍ مُسْلِمٍ بِيَمِينِهِ، فَقَدْ أَوْجَبَ اللهُ لَهُ النَّارَ، وَحَرَّمَ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ» فَقَالَ لَهُ رَجُلٌ: وَإِنْ كَانَ شَيْئًا يَسِيرًا يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «وَإِنْ قَضِيبًا مِنْ أَرَاكٍ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 137]
المزيــد ...
Daga Abu Umama Iyas ɗan Sa'alaba alHarisi - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 137]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar daga yin rantsuwa da Allah akan ƙarya kuma yana sane, hakan dan yankar haƙƙin wani mutum musulmi, domin cewa sakamkon hakan shi ne cancantar wuta, da haramta aljanna, kuma shi yana daga manyan zunubai. Sai wani mutum ya ce ya Manzon Allah: Koda abinda aka rantse akan shi ɗin wani abune dan kaɗan? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Koda hakan ya zama a itacen asuwakin da ake cira ne daga bishiyar ƙirya.