عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم : «لا تَلَقَّوُا الرُّكبان، ولا يبع بعضكم على بيع بعض، ولا تَنَاجَشُوا ولا يبع حَاضِرٌ لِبَادٍ، ولا تُصَرُّوا الإبلَ والغنم، ومن ابتاعها فهو بخير النَّظَرَين بعد أن يحلبها: إن رَضِيَهَا أمسكها، وإن سَخِطَها رَدَّهَا وَصَاعا ًمن تمر».
[صحيح] - [متفق عليه، والرواية الثانية رواها مسلم]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira-Allah ya yarda da shi- daga Annabi : "Ka ku tari hanya, kuma kada dayanku yayi cikin akan cinikin Dan uwansa, kuma kada kuyi keta, kuma kada Mutumin birni ya siyarwa da Mutumin kauye kayansa, kuma kada ku daure hantsar rakuma ko dabbobi"
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi ya hana abubuwa biyarna ciniki harantacce, sabida abn da yake cknsa na cutarwa wanda tana komawa uwa ma saye da mai siiyarwa.1.sai ya hana taran wadanda suka zo don saida kayansa na abinci ko dabbobi, to sa ya tare su kafin suje kasuwa, to sai ya siya daga wurinsu, to sabida basu san yaya kasuwa take ba, sau da yawa sai a danfaresu, kuma ya haramta musu sauran arzikinsu da suka sha wahala akansa. 2. kuma ya hana ciniki kan ciniki daya, kuma kwatankwacin siya kan siyansa, kuma wannan kamar ya ce a cinikin zabin wurin ciniki ko kuma sharadi a cikin ciniki: kamar ya ce zan baka wannan hajar a farashi kasa da yadda ake siyarwa idan Mai saye ne, ko sama da yadda ake siyarwa, ko kuma zan siya da da sama da kudinta, idan shi ne mai siyarwa, don y bata cinikin wani don shi a yi da shi,kuma to irin wannan zabin guda biya, an hanasu a ciniki sabida abinda yake jawowa na barnar abinda zai janyo kullata da gaba da kiyayya, da kuma abinda yake cikinsa na yanke Arzikin Dan uwanka. 3.sannan anyi hani akan kore: shi ne a kara kudin kadara ba tar da niyyar siya ba don a amfanar da mai siyarwa yadda zai samu riba da yawa, ko cutar da mai saya da sanya masa kayan yayi tsada kuma an hana hakan, sabida abinda yake cikinsa na karya da rudi ga mai saye, da kuma daga farashi ta hanayar yaudara da Ha'inci. 4.kuma an hana cinikin Dan kauye da Dan birni ta hanyar ya shige masa gaba wajen siyar da kayan sa domin shi yasan duk farashin kasuwa, ba za'a barwa yan Kasuwa wata kofar cin riba bakuma Annabi yana cewa: "ku kyale Mutane Allah ya Azurta wasu da wasun su". 5. An hana cinikin Daure Hantsa na Dabbobi, ta yadda mai saye a Al'ada yana saye sabida hakan, sai ya siyi Dabbar sama da kudinta kuma alhalin bata kai ba, sai ya zamanto an yaudare shi kuma an alunce shi, sai Shari'a ta sanya masa lokaci da zai iya gano zaluncin da akayi masa, kuma ta bashi zabi kan yayi kwana uku yana rike da Dabbar, kuma yana da dama ya mayar da ita bayan yasan cewa anyi mata Daurin Hantsa to idan ya riga ya tasti nononta sai ya dawo da itada kuma karin kwano daya na Dabino a maimakon nonon.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Portuguese
Manufofin Fassarorin