+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه : «نهى رسول الله صلى الله عليه وسلم أن يبيع حاضرٌ لباد، ولا تناجشوا. ولا يبَعِ ِالرجل على بيع أخيه، ولا يخطب على خطبته ، ولا تسأل المرأة طلاق أختها لتِكْفَأَ ما في صَحفَتِهَا».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi: "Annabi ya hana Dan Gari ya siyarwa da Dan Kauye, (kayansa a Kasuwa), kuma kada kuyi keta, kuma kada wani daga cikinku yayi ciniki akan cinikin Dan Uwansa, kuma kada ya nemi Aure kan neman Auren Dan Uwansa".
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Shari'a tana kwadayin kautar da duk abinda zai jawo gaba ko kiyayya a tsakanin "ya'yan Musulmi, kuma wannan yana bayyane ta hanyar wannan Nassi kamar haka: Annabi ya hana kari akan kudin haja ba tare da niyyar saye ba, don kawai amfanin mai siyarwa ta hanyar kara kudin, ko don cutar da Mai saye da sanya kayan yayi tsada kuma an hana hakan, sabida abinda yake janyowa na karya da kuma rudi da mai saye, da kuma daga Darajar kayan ta hanyar Makirci da yaudara. kuma ya hana Mutumin Birni ya siyarwa da Mutumin kauye kayansa a kasuwa, don shi yasan kudin kayan; ta hanayar haka ya toshe duk kafar da Masu saye zasu ci riba, kuma Annabi yana cewa : "ku bar Mutane sashinsu su Azurta da sashi" kuma idan mai ita ya siyar da kansato mai saye zai samu wani rangwamen da shi ma zai ci riba, don haka aka hana Mutumin Birni ya yiwa mutumin kauye don akwai takurawa ga Mutanen birni, kuma harmta neman Aure akan neman Auren Dan uwansa, har sai yasan cewa Mai neman farko ya fita ko an hana sh, ko ba'a amsa masa ba don sabida neman Aure kan neman Aure abunda yake jawowa na gaba da kuma kiyayya, da kuma jefa kai ga Abinda zai hana Arziki, da kuma hanin Mace kan ta nemi Miji ya saki kishiyarta ko ta cusa masa kinta, ko kuma rigima a tsakaninsu, don ta sanya sharri a tsakaninsu, har yakai sun rabu, to wannan Haram ne, sabida abinda yake cikin ta na Barna mai girma, na gadar da gaba, da janyo fitintunu, da kuma yanke Arzikin wacce aka saka, wanda ya suturtashi da fadin abinda yake cikin kwaryarta na Alkairi wanda Aure ne yake jawo shi, kuma yake wajabta shi akan miji na ciyarwa da kuma tufatarwa, da sauran hakkokin Aure.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin