عن ابن عمر رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم «أنه نهى عن النذر، وقال: إنّ النَّذْرَ لا يأتي بخير، وإنما يُسْتَخْرَجُ به من البخيل».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Dan Umar -Allah ya yarda da su- Daga Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata gare shi- "Lallai ya hana yin Alwashi, yace: Lallai Alwashi ba ya zuwa da alheri, ana fitar da shi daga marowaci ne.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi -tsira da amincin Allah- ya yi hani ga yin Alwashi, dalilin hana yin Alwashin kuwa shi ne ba ya zuwa da alheri, don kuwa yana wajabtawa mutum wani abu da bai zama dole akansa ba tun asali, sai Annabi ya jiye wa wanda ya yi Alwashi tsoron gaza cika shi, hakan kuwa ka iya janyo wa mutum zunubi, hakanan kuma yana kunshe da wani abu mai kama da jingina yin ibada ga musanye da Allah wajen samun abin da ake so, ko gusar da abin da ake ki, wata kila ma mai yinsa ya zaci Allah yana amsa bukatunsa ne don shima ya bautawa Allah -Allah ya kiyaye- Don haka ne Annabi ya hana yin Alwahi don neman sauki, da kuma kwadayin samun kyautar Allah Madaukaki ta hanyar kwadayi da addu'a, ba ta hanyar musanye ko gindaya wani sharadi ba Alwashi bashi da wani amfani, sai dai ana fitar da shi daga marowaci ne, wanda baya yin abin da ke wajibi akanshi, sai dai ya yi shi dole, cikin nawa, ba tare da kyakkyawar niyya ko kwadayin abin da ke wajen Allah Madaukaki ba.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili
Manufofin Fassarorin