عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَرَأَيْتَ إِنْ جَاءَ رَجُلٌ يُرِيدُ أَخْذَ مَالِي؟ قَالَ: «فَلَا تُعْطِهِ مَالَكَ» قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَاتَلَنِي؟ قَالَ: «قَاتِلْهُ» قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَتَلَنِي؟ قَالَ: «فَأَنْتَ شَهِيدٌ»، قَالَ: أَرَأَيْتَ إِنْ قَتَلْتُهُ؟ قَالَ: «هُوَ فِي النَّارِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 140]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son karɓar kuɗina? Ya ce: «Kada ka ba shi kuɗinka)) Ya ce: Shin kana ganin idan ya yaƙe ni? Ya ce: «Ka yaƙe shi» Ya ce: Shin kana ganin idan ya kashe ni? Ya ce: «Kai shahidi ne». Ya ce: Shin kana ganin idan na kashe shi ? Ya ce: «Shi yana cikin wuta»
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 140]
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin idan wani mutum ya zo yana son ƙwatar dukiyata? Ya ce: Bai wajaba ka miƙa wuya ka ba shi dukiyarka ba, ya ce: Shin kana ganin idan ya yaƙeni? Ya ce: Yana halatta gareka ka yaƙe shi, ya ce: Shin kana ganin idan ya kasheni fa? Ya ce: To kai shahidi ne, ya ce: Shin kana ganin idan na kashe shi fa? Ya ce: Shi ya cancanci a yi masa uƙuba a cikin wuta a ranar alƙiyama.