عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَمَّا عُرِجَ بِي مَرَرْتُ بِقَوْمٍ لَهُمْ أَظْفَارٌ مِنْ نُحَاسٍ يَخْمُشُونَ بها وُجُوهَهُمْ وَصُدُورَهُمْ، فَقُلْتُ: مَنْ هَؤُلَاءِ يَا جِبْرِيلُ، قَالَ: هَؤُلَاءِ الَّذِينَ يَأْكُلُونَ لُحُومَ النَّاسِ، وَيَقَعُونَ فِي أَعْرَاضِهِمْ».
[حسن] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 4878]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Lokacin da aka hau da ni (aka yi Mi'iraji da ni) na wuce wasu mutane da suke da farata na tagulla, suna yakusar fuskokinsu da ƙirazansu da su, sai na ce: Su waye waɗannan ya Jibril, ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke cin naman mutane, kuma suke afkawa cikin mutuncinsu».
[Hasan ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi] - [سنن أبي داود - 4878]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa shi: Lokacin da aka hau da shi zuwa sama a daren Isra'i da Mi'iraji, ya wuce wasu mutane suna da farata na tagulla suna yakusa suna yayyaga fuskokinsu da ƙirazansu da su, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya tambayi (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi -: Me waɗannan mutanen suka aikata har ake musu sakayya da wannan azabar? Sai (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya ce: Waɗanan sune waɗanda suke yi da mutane, kuma suke magana a kan mutuncinsu ba tare da gaskiya ba.