عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِيَّاكُمْ وَمُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ، فَإِنَّمَا مَثَلُ مُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ كَقَوْمٍ نَزَلُوا فِي بَطْنِ وَادٍ، فَجَاءَ ذَا بِعُودٍ، وَجَاءَ ذَا بِعُودٍ، حَتَّى أَنْضَجُوا خُبْزَتَهُمْ، وَإِنَّ مُحَقَّرَاتِ الذُّنُوبِ مَتَى يُؤْخَذْ بِهَا صَاحِبُهَا تُهْلِكْهُ».
[صحيح] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 22808]
المزيــد ...
Daga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Na haneku da ƙananan zunibai, kaɗai misalin ƙananan zunubai kamar mutane ne da suka sauka a cikin wani kwari, sai wannan ya zo da ice, wannan ma ya zo da ice, har suka sa gurasarsu ta nuna, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu saboda su zasu halaka shi».
[Ingantacce ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 22808]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga sakaci a aikata ƙananan zunubai, da kuma yawaitasu domin cewa su idan sun taru zasu halakar, kuma ya buga misali akan hakan da wasu mutanen da suka sauka a cikin wani kwari, sai kowanne daga cikinsu ya zo da ita ce ƙarami, har sai da suka sa gurasarsu ta nuna saboda taruwar abinda suka tara na itatuwan, kuma lallai ƙananan zunubai a duk lokacin da aka kama mai aikatasu da su bai tuba daga garesu ba ko kuma Allah bai yi masa afuwa ba to zasu halaka shi.