عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«لاَ يَزَالُ قَلْبُ الكَبِيرِ شَابًّا فِي اثْنَتَيْنِ: فِي حُبِّ الدُّنْيَا وَطُولِ الأَمَلِ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6420]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Zuciyar babba ba zata gushe ba tana budurwa a kan abubuwa biyu: A son duniya da tsawon buri".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6420]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dattijo yana girma jikinsa yana rauni, sai dai zuciyarsa budurwa ce akan son abubuwa biyu: Na farko: Son duniya da yawan dukiya. Na biyu: Tsawon rayuwa da shekaru da buri.