عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«بَدَأَ الْإِسْلَامُ غَرِيبًا، وَسَيَعُودُ كَمَا بَدَأَ غَرِيبًا، فَطُوبَى لِلْغُرَبَاءِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 145]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Musulunci ya fara yana baƙo, kuma zai dawo baƙo, aljanna ta tabbata ga baƙi».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 145]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Musulunci ya fara yana baƙo a cikin ɗaiɗaikun mutane da kuma ƙarancin ma'abotansa, kuma zai dawo yana baƙo saboda ƙarancin wanda zai tsayu da shi, to farin ciki, kuma madalla ga baƙi, da farin ciki da sanyin ido gare su.