+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«أَكْثِرُوا ذِكْرَ هَادمِ اللَّذَّاتِ» يَعْنِي الْمَوْتَ.

[حسن] - [رواه الترمذي والنسائي وابن ماجه] - [سنن ابن ماجه: 4258]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa.

[Hasan ne] - - [سنن ابن ماجه - 4258]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yawaita tinanin mutuwa, da tinaninta ne mutum yake tuna lahira, kuma soyayyarsa ga duniya ta rushe a cikin zuciyarsa, musammanma dai abubuwan da aka haramta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Mutuwa tana yanke jin daɗin duniya, sai dai a haƙƙin mumini tana dago shi zuwa jin daɗin lahira da jin daɗin aljanna da abinda yake faruwa a cikinta na alheri mai girma.
  2. Tina mutuwa da abinda ke bayanta yana daga sabubban tuba da barin laifi da kuma tanadi dan lahira.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin