عَنْ أَبِي مُوسَى رضي الله عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّمَا مَثَلُ الْجَلِيسِ الصَّالِحِ وَالْجَلِيسِ السَّوْءِ كَحَامِلِ الْمِسْكِ وَنَافِخِ الْكِيرِ، فَحَامِلُ الْمِسْكِ: إِمَّا أَنْ يُحْذِيَكَ، وَإِمَّا أَنْ تَبْتَاعَ مِنْهُ، وَإِمَّا أَنْ تَجِدَ مِنْهُ رِيحًا طَيِّبَةً، وَنَافِخُ الْكِيرِ: إِمَّا أَنْ يُحْرِقَ ثِيَابَكَ، وَإِمَّا أَنْ تَجِدَ رِيحًا خَبِيثَةً».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2628]
المزيــد ...
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi, maɗaukin alimiski: Kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ƙanshi mai daɗi daga gare shi, mai busa zugazugi kuwa: Kodai ya ƙona kayanka, ko kuma ka samu mummunan ƙanshi daga gare shi".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2628]
Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya buga misali ga nau'i biyu na mutane:
Nau'i na farko: Abokin zama da aboki na gari wanda yake shiryarwa ga Allah a abinda a cikinsa akwai yardar Allah, kuma yana taimakawa akan biyayya ga Allah, To kwatankwacinsa kamar mai saida almiski ne, kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ka shaƙi ƙanshi mai daɗi daga gare Shi.
Nau'i na biyu: Abokin zama kuma mummunan aboki; wanda yake toshe tafarkin Allah, kuma yana taimako akan aikin saɓo, kuma kana ganin mummunan aiki daga gare shi, kuma yana tsawaita maka zargi dan abokantaka da zama da irinsa, to kwatankwacinsa kamar maƙeri ne wanda yake hura wutarsa; kodai ya ƙona maka tufafi daga tartsatsinsa mai tashi, ko ka samu mummunan wari saboda kusantakarsa.