عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الخُدْرِيِّ رضي الله عنه أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ مِنْ أَعْظَمِ الجِهَادِ كَلِمَةَ عَدْلٍ عِنْدَ سُلْطَانٍ جَائِرٍ».
[حسن لغيره] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 2174]
المزيــد ...
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki".
[Hasan ne ta wani Sanadin] - - [سنن الترمذي - 2174]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga mafi girma da anfanin nau'ikan jihadi a tafarkin Allah - Madaukakin sarki - shi ne kalma ta adalci da gaskiya a wurin azzalumin sarki (shugaba); domin cewa shi aiki ne da alama ce ta horo da aikin alheri da hani daga mummuna, daidai ne ya kasance da fada ne ko rubutu ko aikatawa ko wanin hakan wanda maslaha zata tabbata da shi kuma barna ta tunkude barna.