عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«إِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فُتِّحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ، وَغُلِّقَتْ أَبْوَابُ النَّارِ، وَصُفِّدَتِ الشَّيَاطِينُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1079]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1079]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa idan watan Ramadan ya shiga sai al'amura uku su faru: Na farko: Za'a buɗe ƙofofin aljanna ba za'a kulle wata ƙofa ba daga cikinsu. Na biyu: Za'a kulle ƙofofin wuta, kuma ba za'a buɗe wata ƙofa daga cikinsu ba. Na uku: Za'a ɗaure shaiɗanu da aljanu masu tsaurin kai da sarƙoƙi, ba zasu kai zuwa ga abinda suke tsira da shi a cikin wanin (watan) Ramadan ba. Dukkanin wannan dan girmamawa ne ga wannan watan, da kwaɗaitar da masu aiki akan yawaita ayyukan ɗa'a na sallah da sadaka da zikiri da karatun Alkur'ani da wanin haka; da kuma nisantar zunubai da saɓo.