عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«قَالَ اللَّهُ: كُلُّ عَمَلِ ابْنِ آدَمَ لَهُ، إِلَّا الصِّيَامَ، فَإِنَّهُ لِي وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، وَالصِّيَامُ جُنَّةٌ، وَإِذَا كَانَ يَوْمُ صَوْمِ أَحَدِكُمْ فَلاَ يَرْفُثْ وَلاَ يَصْخَبْ، فَإِنْ سَابَّهُ أَحَدٌ أَوْ قَاتَلَهُ، فَلْيَقُلْ إِنِّي امْرُؤٌ صَائِمٌ، وَالَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ، لَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ المِسْكِ، لِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ يَفْرَحُهُمَا: إِذَا أَفْطَرَ فَرِحَ، وَإِذَا لَقِيَ رَبَّهُ فَرِحَ بِصَوْمِهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1904]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi, azimi garkuwa ne, idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa kada ya yi zancen banza, idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi, to ya ce lallai ni mai azimi ne, na rantse da wanda ran (Annabi) Muhammad yake a hannunSa, bashin bakin mai azimi shi ne mafi ɗaɗi a wurin Allah daga ƙanshin almiski, mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki, kuma idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1904]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana faɗa a cikin Hadisi Ƙudsi:
Dukkan aikin Ɗan Adam ana ninka kyakkyawa da kwatankwacinsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, sai azimi; shi nawa ne riya ba ta shiga cikinsa, kuma nine zan yi sakayya da shi, sai in kaɗaita da sanin gwargwadan ladansa da kuma ninka kyawawan (ladansa).
Sannan Ya ce: (Azimi garkuwa ne) kuma kariya ne kuma sitira ne kuma katanga ne mai katangewa daga wuta; domin cewa shi kamewa ne daga sha'awowi da afkawa cikin zunubai, wuta kuma abar kewayewa ce da sha'awowi.
(Idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa) da yin jima'i da abubuwan gabatarwarsa, ko mummunan zance kai tsaye.
(Kada ya yi zancen banza) da yin husuma da kuma kururuwa.
(Idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi) a cikin Ramadan to ya ce: Lallai ni mai azimi ne; wataƙila ya ƙyale shi, idan ya nace sai dai faɗa to a haƙiƙa to sai ya tunkuɗe shi da mafi sauƙi, sai mafi sauƙi kamar wanda ya shigo maka gida.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi rantsuwa da wanda ransa yake a hannunSa cewa canzawar bashin bakin mai azimi saboda azimin ya fi daɗi a wurin Allah ranar alƙiyama daga ƙanshin almiski a wurinku, kuma ya fi yawan lada daga almiski abin so gare shi a ranakun juma'a da kuma majalisan zikiri.
Mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su:
Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki da gushewar yunwarsa da kuma ƙishirwarsa saboda yadda aka halatta masa buda baki.
Kuma zai yi farin ciki da cikar aziminsa da kuma kammala bautarsa, da kuma sauƙi daga Ubangijinsa, da taimako akan aziminsa na gaba.
(Idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa) da sakamakonsa da kuma ladansa.