عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «من صَام رمضان إيِمَانًا واحْتِسَابًا، غُفِر له ما تَقدَّم من ذَنْبِه».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...
Daga Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - da isnadi: "Duk wanda ya azumci Ramadan saboda imani da hisabi, za a gafarta masa zunubansa na baya."
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
Ma'anar hadisin: Cewa duk wanda ya azumci watan Ramadhan saboda imani da Allah, tabbatar da alkawarinsa, la'akari da ladarsa, niyya zuwa ga Allah Madaukaki - ba tare da riya ko suna ba, za a gafarta masa zunubansa da suka gabata.