عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه مرفوعاً: «يا معشر الشباب، من استطاع منكم الباءة فليتزوج؛ فإنه أغض للبصر، وأحصن للفرج، ومن لم يستطع فعليه بالصوم؛ فإنه له وِجَاءٌ».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi "Ya ku Matasa, kuma duk wanda yake da iko daga cikinku to yayi Aure; domin cewa shi ne mafi kariya ga idanunsa, kuma shi ne mafi ;kariya ga al'aurarsa, kuma duk wanda bai sami iko ba to yayi Azumi domin Azumi garkuwa ne a gare shi'
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Sabida cewa lallai Katangewa da kuma kamewa Wajibi ne, kuma akasinsu Haramun ne, kuma yana zuwa ne ta hanayar tsananin sha'awa tare da raunin Imani, kuma samartaka tafi tsananin Sha'awa, sai Annabiya yi musu magana yana mai shiryar da su izuwa hanayar kamewa, wanda hakan cewa duk wanda ya sami abinda zai iya yin Aure na Sadaki, da kuma ciyarwa, to yayi Aure domin Aure yana iya kare masa ganinsa ga barin Haram, kuma yana iya katange musu Al'aurarsu ga barin Al'fasha, kuma ya kwadaitar da wanda bashi da iko ba kuma yana da sha'awar Auren to da yayi ta Azumi, don yana da lada, kuma zai kame masa Sha'awarsa, da kuma ninkinta da barin Abincida kuma yawan sha, sai jiki yayi rauni kuma Magudanan Jini da Shaidan yake binsu su toshe, kuma Azumi yana karya sha'awa Kamar garkuwa ne ga kwayoyin halittar da suke gyara Maniyyi sai ta tayar da Sha'awa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin