عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«يَسِّرُوا وَلَا تُعَسِّرُوا، وَبَشِّرُوا وَلَا تُنَفِّرُوا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 69]
المزيــد ...
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 69]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da umarnin sauƙaƙawa da rangwame wa mutane, da kada a tsananta musu a dukkanin lamura na addini da na rayuwa, wannan kuwa a daidai yadda Allah Ya halatta Ya kuma shar’anta.
Kuma yana kwaɗaitarwa a kan bushara da alheri, da rashin korar (kyarar) mutane.