عَنْ سَهْلٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِنَّ فِي الْجَنَّةِ بَابًا يُقَالُ لَهُ الرَّيَّانُ، يَدْخُلُ مِنْهُ الصَّائِمُونَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ، لَا يَدْخُلُ مِنْهُ أَحَدٌ غَيْرُهُمْ، يُقَالُ: أَيْنَ الصَّائِمُونَ، فَيَقُومُونَ لَا يَدْخُلُ مِنْهُ أَحَدٌ غَيْرُهُمْ، فَإِذَا دَخَلُوا أُغْلِقَ، فَلَمْ يَدْخُلْ مِنْهُ أَحَدٌ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1896]
المزيــد ...
Daga Sahl - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai a cikin aljanna akwai wata ƙofa ana kiranta Rayyanu, masu azumi ne za su shiga ta cikin ta a ranar Alƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba, za'a ce: Ina masu azumi? sai su tashi, babu wanda zai shiga ta nan in ba su ba, idan suka shige za'a kulleta, ba wanda zai shiga ta ita".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1896]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa akwai wata ƙofa daga cikin ƙofofin aljanna ana kiranta: Kofar Rayyan, masu azimi zasu shigeta ranar alƙiyama, babu wanda zai shiga (aljanna) ta kofar sai su, za’a yi kira: Ina masu azimi, sai su miƙe su shiga, waninsu ba zai shiga ba, idan na ƙarshensu ya shiga sai akulleta, babu wani da zai shiga bayan nan.