عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِذَا لَقِيَ أَحَدُكُمْ أَخَاهُ فَلْيُسَلِّمْ عَلَيْهِ، فَإِنْ حَالَتْ بَيْنَهُمَا شَجَرَةٌ أَوْ جِدَارٌ أَوْ حَجَرٌ ثُمَّ لَقِيَهُ فَلْيُسَلِّمْ عَلَيْهِ أَيْضًا».
[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 5200]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce :
"Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma".
[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 5200]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da musulmi da yin sallama ga ɗan uwansa musulmi duk lokacin da ya haɗu da shi, koda sun kasance suna tafiya tare ne kuma wani abu mai rabawa ya raba su, kamar bishiya ko gini ko babban dutse, sannan ya haɗu da shi bayan nan to ya yi masa sallama karo na biyu.