+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا تَقَدَّمُوا رَمَضَانَ بِصَوْمِ يَوْمٍ وَلَا يَوْمَيْنِ إِلَّا رَجُلٌ كَانَ يَصُومُ صَوْمًا فَلْيَصُمْهُ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1082]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1082]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya yi azimi kafin Ramadan da yini ɗaya ko yini biyu akan niyyar lissafa shi a (watan) Ramadan; domin wajabacin azimin Ramadan an rataya shi ne da ganin jinjirin wata, babu buƙatuwa ga ɗorawa kai, sai dai wani wanda ya kasance yana yin wani azimin da ya sabayi kamar azimin yini da fashin yini (irin na annabi Dawud), ko ranar litinin ko alhamis sai ya yi daidai da shi to ya azimce shi; wannan bai zamo daga tarbar Ramadan a wani abu ba, an riskar da hakan abinda ya kasance azimi ne na wajibi kamar ramuwa da bakance.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hani daga ɗorawa kai (wahala), da wajabcin kiyayewa akan ibada kamar yadda aka shara'antata ba tare da ƙari ko ragi ba.
  2. Daga hikimar hakan - Allah ne Mafi sani - banbance farillan ibadu daga nafilfilinsu, da yi wa Ramadan tanadi da nishaɗi da kwaɗayi, kuma dan azimi ya zama alamar wannan watan mai falala abin banbancewa da shi.