عَنْ أَبِي عُبَيْدٍ، مَوْلَى ابْنِ أَزْهَرَ، قَالَ:
شَهِدْتُ العِيدَ مَعَ عُمَرَ بْنِ الخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، فَقَالَ: هَذَانِ يَوْمَانِ نَهَى رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ صِيَامِهِمَا: يَوْمُ فِطْرِكُمْ مِنْ صِيَامِكُمْ، وَاليَوْمُ الآخَرُ تَأْكُلُونَ فِيهِ مِنْ نُسُكِكُمْ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1990]
المزيــد ...
Daga Abu Ubaid, 'yantaccen Ibnu Azhar, ya ce:
Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1990]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani game da azimin ranar idin ƙaramar sallah da idin babbar sallah; amma idin ƙaramar sallah to ranar buɗa baki ce daga azimin watan Ramadan, amma ranar idin babbar sallah to ranar ci ce daga abubuwan layya.