عَنْ ابْنَ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِذَا رَأَيْتُمُوهُ فَصُومُوا، وَإِذَا رَأَيْتُمُوهُ فَأَفْطِرُوا، فَإِنْ غُمَّ عَلَيْكُمْ فَاقْدُرُوا لَهُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1900]
المزيــد ...
Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1900]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana alamar shigar watan Ramadan da kuma fitarsa, sai ya ce: Idan kun ga injirin watan Ramadan to ku azimce shi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwanaki talatin na watan Sha'aban, idan kun ga jinjirin watan Shawwal to ku ajiye azumi, idan girgije ya tsare tsakaninku da shi ya ɓuya gareku; to ku ƙirga kwana talatin ga watan Ramadan.