عَنْ زِرِّ بْنِ حُبَيْشٍ قَالَ:
أَتَيْتُ صَفْوَانَ بْنَ عَسَّالٍ المُرَادِيَّ، أَسْأَلُهُ عَنِ المَسْحِ عَلَى الخُفَّيْنِ، فَقَالَ: مَا جَاءَ بِكَ يَا زِرُّ؟ فَقُلْتُ: ابْتِغَاءَ العِلْمِ، فَقَالَ: إِنَّ المَلاَئِكَةَ لَتَضَعُ أَجْنِحَتَهَا لِطَالِبِ العِلْمِ؛ رِضًا بِمَا يَطْلُبُ، فَقُلْتُ: إِنَّهُ حَكَّ فِي صَدْرِي المَسْحُ عَلَى الخُفَّيْنِ بَعْدَ الغَائِطِ وَالبَوْلِ، وَكُنْتَ امْرَأً مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَجِئْتُ أَسْأَلُكَ: هَلْ سَمِعْتَهُ يَذْكُرُ فِي ذَلِكَ شَيْئًا؟ قَالَ: نَعَمْ، كَانَ يَأْمُرُنَا إِذَا كُنَّا سَفْرًا أَوْ مُسَافِرِينَ أَلَّا نَنْزِعَ خِفَافَنَا ثَلاَثَةَ أَيَّامٍ وَلَيَالِيهِنَّ إِلَّا مِنْ جَنَابَةٍ، لَكِنْ مِنْ غَائِطٍ وَبَوْلٍ وَنَوْمٍ، فَقُلْتُ: هَلْ سَمِعْتَهُ يَذْكُرُ فِي الهَوَى شَيْئًا؟ قَالَ: نَعَمْ، كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ فَبَيْنَا نَحْنُ عِنْدَهُ إِذْ نَادَاهُ أَعْرَابِيٌّ بِصَوْتٍ لَهُ جَهْوَرِيٍّ: يَا مُحَمَّدُ، فَأَجَابَهُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى نَحْوٍ مِنْ صَوْتِهِ: «هَاؤُمُ» وَقُلْنَا لَهُ: وَيْحَكَ اغْضُضْ مِنْ صَوْتِكَ، فَإِنَّكَ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، وَقَدْ نُهِيتَ عَنْ هَذَا، فَقَالَ: وَاللَّهِ لاَ أَغْضُضُ، قَالَ الأَعْرَابِيُّ: المَرْءُ يُحِبُّ القَوْمَ وَلَمَّا يَلْحَقْ بِهِمْ، قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «المَرْءُ مَعَ مَنْ أَحَبَّ يَوْمَ القِيَامَةِ»، فَمَا زَالَ يُحَدِّثُنَا حَتَّى ذَكَرَ بَابًا مِنْ قِبَلِ المَغْرِبِ مَسِيرَةُ عَرْضِهِ، أَوْ يَسِيرُ الرَّاكِبُ فِي عَرْضِهِ أَرْبَعِينَ أَوْ سَبْعِينَ عَامًا.
[صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 3535]
المزيــد ...
Daga Zirr Dan Hubaish ya ce:
Na zo wurin Sufwan bn Assal al-Muradi - Allah Ya yarda da shi - ina tambayarsa game da shafa akan huffi, sai ya ce: Meke tafe da kai ya Zir? Sai na ce: Dan neman ilimi, sai ya ce: Lallai Mala'iku suna shimfiɗa fukafukansu ga mai neman ilimi, dan yarda da abinda yake nema, sai na ce: Lallai shafa akan huffi bayan gayaɗi da bawali ya sosu a cikin zuciyata, kai kuma mutum ne daga cikin sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na zo ina tambayarka: Shin ka ji shi yana faɗin wani abu a cikin hakan? Ya ce: Eh, Ya kasance yana umartarmu idan mun kasance a halin tafiya ko matafiya cewa kada mu cire huffinanmu kwanaki uku da dararensu sai dan janaba, amma bahaya da fitsari da bacci (to a'a), sai na ce: Shin ka ji shi yana faɗin wani abu a sha'anin soyayya? ya ce: Eh, mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a halin tafiya lokacin muna wurinsa sai wani balaraben ƙauye ya kira shi da babbar murya: Ya Muhammad, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa gwargwadan muryarsa: «Haum» kuma mukace da shi: Kaicanka ka ƙanƙanta muryarka, lallai kai kana wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -:, alhali an hanaka wannan, sai ya ce: Wallahi bazan ƙanƙar da muryata ba, balaraben ƙauyen ya ce: Mutum yana son mutane amma bai risku da su ba, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: ya ce: «Mutum yana tare da wanda ya so a ranar alƙiyama» bai gushe ba yana zantar da mu har sai da ya ambaci wata ƙofa a ɓangaren yamma, tafiyar faɗinta, ko mahayi zai yi tafiya a faɗinta tsawon shekara arba'in ko saba'in.
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 3535]
Zir bn Hubaish ya zo wurin Safwan bn Assal - Allah Ya yarda da shi -, yana tambayarsa game da shafa akan huffi, sai Safwan ya ce: Meke tafe da kai ya Zir? sai ya ce: Dan neman ilimi, sai ya ce: Lallai mala'iku suna shimfiɗa fukafukansu ga mai neman ilimi; dan yarda da girmamawa ga abin da mai neman ilimi yake aikatawa, sai Zir ya ce: Lallai shafa akan huffi bayan gayaɗi ko fitsari ya yi kai kawo a cikin zuciyata, alhali kai kana daga cikin sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - shi ya sa nazo ina tambayarka shin ka ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗi wani abu a kan haka? Safwan ya ce: Eh, ya kasance yana umartarmu idan mun kasance matafiya kada mu cire huffunanmu tsawon kwana uku da dararensu saboda hadasi ƙarami, kamar gayaɗi da fitsari da bacci, sai dai saboda janaba kawai, to ya wajaba a cire, sai na ce: Shin ka ji shi ya faɗi wani abu game da so? Ya ce: Eh, mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wata tafiya mun kasance muna wurinsa sai ga wani balaraben ƙauye ya kira shi da babbar murya: Ya Muhammad, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya amsa masa da babbar murya kusa da muryarsa: Zo, sai mukace masa: Kaicanka ka ƙanƙar da muyarka, kaifa kana wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali an hanaka ɗaga murya a wurinsa. Saboda kakkausan halinsa sai ya ce: Wallahi ba zan ƙanƙar da muryar ba, sai balaraben ƙauyen ya ce: Ya Manzon Allah, mutum yana son mutane nagari amma bai yi irin aikinsu ba? Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Mutum yana tare da wanda ya so a ranar alƙiyama, Zir ya ce: Safwan bai gushe ba yana zantar da mu har sai da ya ambaci wata ƙofar tuba a ɓangaren Sham, Allah Ya halicceta ranar halittar sammai da ƙasa, mahayi zai yi tafiya a faɗinta tsawon shekara arba'in ko saba'in, kuma ba za'a kulleta ba har sai rana ta ɓullo ta yammacinta.