عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إِذَا تَوَضَّأَ أَحَدُكُمْ وَلَبِسَ خُفَّيْهِ فَلْيُصَلِّ فِيهِمَا، وَلْيَمْسَحْ عَلَيْهِمَا ثُمَّ لَا يَخْلَعْهُمَا إِنْ شَاءَ إِلَّا مِنْ جَنَابَةٍ».
[صحيح] - [رواه الدارقطني] - [سنن الدارقطني: 781]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa akansu, sannan kada ya ciresu in ya so sai dai saboda janaba".
[Ingantacce ne] - [Al-Dar Al-Kutni Ya Rawaito shi] - [سنن الدارقطني - 781]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa idan musulmi ya sanya huffinsa bayan ya yi alwala, sannan ya kari (hadasi) bayan nan kuma ya yi nufin alwala, to yana da damar yin shafa akansu idan ya yi nufin hakan, kuma ya yi sallah da su kada ya ciresu a wani sanannen lokaci, sai dai idan ya samu janaba to cire huffin ya wajaba a gare shi saboda yin wanka.