+ -

عَنْ حُذَيْفَةَ رضي الله عنه قَالَ:
كُنْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَانْتَهَى إِلَى سُبَاطَةِ قَوْمٍ، فَبَالَ قَائِمًا، فَتَنَحَّيْتُ فَقَالَ: «ادْنُهْ» فَدَنَوْتُ حَتَّى قُمْتُ عِنْدَ عَقِبَيْهِ فَتَوَضَّأَ فَمَسَحَ عَلَى خُفَّيْهِ.

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 273]
المزيــد ...

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
"Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye, sai na yi nesa, sai ya ce: "ka kusanto" sai na kusanto har na tsaya daura da maƙyangymansa sai ya yi alwala sai ya yi shafa akan kuffinsa biyu.

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 273]

Bayani

Huzaifa Dan Yaman - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa shi ya kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya so ya yi fitsari, sai ya shiga jujin wasu mutane; shi ne gurin da ake zubar da tsummokara da sharar da ake sharewa a cikin gidaje, sai ya yi fitsari alhali shi yana tsaye, ya kasance mafi yawancin al'adarsa shi ne ya yi fitsari a zaune.
Sai Huzaifa ya yi nesa da shi, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce masa: Ka kusanto, sai Huzaifa ya kusanto gare shi har ya tsaya a bayansa daura da ƙarshen diga-digansa; dan ya zama kamar kariya gare shi daga kallonsa a wannan halin.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi alwala, lokacin wanke ƙafafuwansa biyu, sai ya wadatu da shafa akan kuffinsa biyu - su ne abinda ake ɗaurawa a ƙafa na fata mara kauri da makamancinta kuma yana zama mai suturce idan sawu - kuma bai ciresu ba.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Halaccin shafa akan kuffi biyu.
  2. Halaccin yin fitsari a tsaye da sharaɗin kada wani fitsarin ya same shi.
  3. Yadda annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agre shi - ya nemi juji, shi ne bola da shara domin cewa su a galibi masu sauƙi ne fitsari ba zai dawowa mai yin fitsarin ba.