عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنه:
أَنَّهُ لَقِيَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي طَرِيقٍ مِنْ طُرُقِ الْمَدِينَةِ وَهُوَ جُنُبٌ، فَانْسَلَّ فَذَهَبَ فَاغْتَسَلَ، فَتَفَقَّدَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَلَمَّا جَاءَهُ قَالَ: «أَيْنَ كُنْتَ يَا أَبَا هُرَيْرَةَ؟» قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، لَقِيتَنِي وَأَنَا جُنُبٌ فَكَرِهْتُ أَنْ أُجَالِسَكَ حَتَّى أَغْتَسِلَ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «سُبْحَانَ اللهِ، إِنَّ الْمُؤْمِنَ لَا يَنْجُسُ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 371]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da shi a wata hanya cikin hanyoyin Madina alhali shi yana da janaba, sai ya sulale ya tafi ya yi wanka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bibiye shi, lokacin da ya zo masa sai ya ce: «Ina kake ya Abu Huraira?» sai ya ce: Ya Manzon Allah ka haɗu da ni alhali ni ina da janaba sai na ƙyamaci in zauna da kai har sai na yi wanka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 371]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - a sashin hanyoyin Madina, Abu Huraira ya kasance yana da janaba, kuma yana daga cikin girmamawarsa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ƙyamaci zama da shi da kuma hira da shi alhali shi yana kan wannan halin dan yana zatan cewa shi najasa ne, sai ya tafi a ɓoye ya yi wanka, sannan ya dawo, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye shi ina ya tafi? Sai ya sanar da shi halin da yake ciki, kuma cewa shi ya ƙyamaci zama da shi ne alhali shi yana najasa saboda janabar (da ta same shi), sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mamaki kuma ya ce masa: Lallai cewa mumini mai tsarki ne ba ya zama najasa akan kowane hali; a raye ko a mace.