عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَا تَحَاسَدُوا، وَلَا تَنَاجَشُوا، وَلَا تَبَاغَضُوا، وَلَا تَدَابَرُوا، وَلَا يَبِعْ بَعْضُكُمْ عَلَى بَيْعِ بَعْضٍ، وَكُونُوا عِبَادَ اللهِ إِخْوَانًا الْمُسْلِمُ أَخُو الْمُسْلِمِ، لَا يَظْلِمُهُ وَلَا يَخْذُلُهُ، وَلَا يَحْقِرُهُ التَّقْوَى هَاهُنَا» وَيُشِيرُ إِلَى صَدْرِهِ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ «بِحَسْبِ امْرِئٍ مِنَ الشَّرِّ أَنْ يَحْقِرَ أَخَاهُ الْمُسْلِمَ، كُلُّ الْمُسْلِمِ عَلَى الْمُسْلِمِ حَرَامٌ، دَمُهُ، وَمَالُهُ، وَعِرْضُهُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2564]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalince shi kuma kada ya ƙi taimakonsa, kada ya wulaƙanta shi tsoron Allah a nan yake" - ya yi nuni zuwa ƙirjin sa, sau uku - "Ya ishi mutum sharri ya wulaƙanta ɗan uwansa musulmi, kowane musulmi akan musulmi haramun ne (ya zubda) jininsa, da dukiyarsa da mutuncinsa". Mutuncinsa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2564]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa musulmi wasiyya ta alheri ga ɗan'uwansa musulmi, kuma ya bayyana sashin abinda yake wajaba akansa na wajibai da ladubba daura da su; daga hakan: Wasiyya ta farko: Kada ku yi wa juna hassada, ita ce sashinku ya yi burin gushewar ni'imar sashi. Na biyu: Kada ku yi cinikin koɗe shi ne mutumin da ba ya nufin yin siyan abin siyan sai ya yi ƙari a farashin abin siyan; kawai yana nufin anfanar mai siyarwar, ko cutar da mai siyan. Na uku: Kada ku yi ƙiyayya, ita ce nufin shigar da cuta kuma ita ce kishiyar soyayya; sai dai idan ƙiyayyar ta kasance ne a lamarin Allah ne - Maɗaukakin sarki -; to shi wajibi ce. Na huɗu: Kada ku juyawa juna baya, shi ne kowane ɗaya daga cikinku ya juyawa ɗan'uwansa bayansa da ƙeyarsa sai ya bijire masa kuma ya ƙaurace masa. Na biyar: Kada sashinku ya yi ciniki akan cinikin sashi, shi ne yacewa mai siyan: A wurina akwai irinta da ƙasa da farashinta ko ta fita kyau kuma farashinta bai kai nata ba. Sannan tsira da aminci su tabbata a gare shi ya yi wasiyya da wasiyya mai tattaro (ma'anoni da hikimomi masu yawa) sai ya ce: Ku zama kamar 'yan'uwa ta hanyar barin abubuwan da aka hana, da kuma nuna soyayya da sassauci da tausayi da sauƙaƙawa da taimakekeniya a aikin alheri, tare da tsarkakakkiyar zuciya da kuma yin nasiha a kowane hali. Daga abinda wannan 'yan uwantakar take hukuntawa: Kada ya zalinci ɗan'uwansa musulmi kuma ya yi ta'addanci akansa. Kada ya bari a zalinci ɗan'uwansa sai ya ƙi taimakonsa a gurin da yake da ikon ya taimake shi, kuma ya ɗauke masa zalincin. Kuma kada ya wulaƙanta shi ya raina shi ya dinga kallonsa da kallo na raini da izgili; shi mai fitowa ne daga girman kai a cikin zuciya. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana har sau uku cewa tsoron Allah a cikin zuciya yake, wanda a cikin zuciyarsa akwai tsoron Allah wanda yake hukunta kyakkyawar ɗabi'a, da tsoron Allah da muraƙabarSa to cewa shi ba zai wulaƙanta musulmi ba, kuma ya ishe shi ɗabi'u na sharri da ƙasƙanci ya wulaƙanta ɗan'uwansa musulmi, hakan saboda girmankan dake cikin zuciyarsa. Ya Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa kan abinda ya wuce cewa kowane musulmi akan musulmi haramun ne: jininsa: Shi ne ya yi masa ta'addanci da kisa ko abinda bai kai kisa ba kamar rauni ko duka da makamancinsu, haka nan dukiyarsa: Shi ne ya ci dukiyar ba tare da wani haƙƙi ba, haka nan mutuncinsa: Shi ne ya zarge shi a kansa ko tsareshi.