Karkasawa: Aqida . Imani da Ranar Lahira .

عَنْ ‌عَائِشَةَ رضي الله عنها:
أَنَّ رَجُلًا قَعَدَ بَيْنَ يَدَيِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ لِي مَمْلُوكِينَ يَكْذِبُونَنِي وَيَخُونُونَنِي وَيَعْصُونَنِي، وَأَشْتُمُهُمْ وَأَضْرِبُهُمْ، فَكَيْفَ أَنَا مِنْهُمْ؟ قَالَ: «يُحْسَبُ مَا خَانُوكَ وَعَصَوْكَ وَكَذَّبُوكَ وَعِقَابُكَ إِيَّاهُمْ، فَإِنْ كَانَ عِقَابُكَ إِيَّاهُمْ بِقَدْرِ ذُنُوبِهِمْ كَانَ كَفَافًا، لَا لَكَ وَلَا عَلَيْكَ، وَإِنْ كَانَ عِقَابُكَ إِيَّاهُمْ دُونَ ذُنُوبِهِمْ كَانَ فَضْلًا لَكَ، وَإِنْ كَانَ عِقَابُكَ إِيَّاهُمْ فَوْقَ ذُنُوبِهِمُ اقْتُصَّ لَهُمْ مِنْكَ الْفَضْلُ»، قَالَ: فَتَنَحَّى الرَّجُلُ فَجَعَلَ يَبْكِي وَيَهْتِفُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَمَا تَقْرَأُ كِتَابَ اللهِ: {وَنَضَعُ الْمَوَازِينَ الْقِسْطَ لِيَوْمِ الْقِيَامَةِ فَلا تُظْلَمُ نَفْسٌ شَيْئًا}، الْآيَةَ»، فَقَالَ الرَّجُلُ: وَاللهِ يَا رَسُولَ اللهِ، مَا أَجِدُ لِي وَلهُمْ شَيْئًا خَيْرًا مِنْ مُفَارَقَتِهِمْ، أُشْهِدُكَ أَنَّهُمْ أَحْرَارٌ كُلُّهُمْ.

[ضعيف] - [رواه الترمذي]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita -
Cewa wani mutum ya zauna a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah ! ina da bayi biyu suna yi mini karya suna ha'intata suna saba mini, ni kuma ina zaginsu ina dukansu, ya matsayina yake garesu (a urin Allah?) Ya ce: "Za'a kirga a binda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, da kuma ukubar da ka yi musu, idan ukubar da ka yi musu gwargwadan laifinsu ne, ya zama daidai wa daida, babu komai gareka ko akanka. Idan ukubar ka akansu kasa da laifin su ne to ya zama falala gareka, idan ukubarka garesu sama da laifin su ne za’a yi masu sakayyar karin daga gareka", ya ce: Sai mutumin yadan yi nesa sai ya fara kuka yana kururuwa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin ba ka karanta littafin Allah ba: {zamu sanya ma'auni na adalci ga yinin Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abu ba}. karanta zuwa karshenta, sai mutumin ya ce; Wallahi ya Manzon Allah, ban ji wani abu gareni dasu ba mafi alheri daga rabuwa da su, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne gaba dayansu.

Ingantacce ne - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi

Bayani

Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana karar halin bayinsa, cewa su suna yi masa karya a labari, suna ha'intarsa a amana, suna yin algus a mu'amala, suna saba masa a al'amari, shi kuma yana zaginsu yana dukansu dan ladabtar da su, sai ya tambaye shi game da halinsa ranar Alkiyama tare da su? sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Za'a lissafa abinda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, kuma za'a lissafta ukubarka garesu, idan gwargwadan ukubar ta yi daidai da laifukansu to ba ka da komai, kuma babu komai a kanka, idan kuma gwargwadan ukubarka garesu kasa da laifukansu ne, ya zama falala da kari gareka a lada, idan ukubarka garesu sama da laifukansu ne za’a yi maka ukuba, za'a karbi gwargwadan karin daga gareka za'a ba su, sai mutumin yadan yi nisa ya fara kuka muryarsa tana sama, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce masa: Shin ba ka karanta littafin Allah ba; {zamu sanya ma'auni na adalci ga ranar Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abuba, idan ya kasance kwatankwacin kwayar komayya ne zamu zo da ita, mun isa zama masu hisabi] [Al-Anbiya;47], ba za’a zalinci wani mutum wani abu ba ranar Alkiyama, kuma ma'aunai za su zama a tsakanin mutane da adalci, sai mutumin ya ce: Wallahi ya manzon Allah, ban ji komai game da ni da su ba sama da na rabu dasu da barinsu, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne sabo da Allah gaba dayansu; dan tsoron hisabi da azaba.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Gaskiyar sahabi a 'yan tawarsa ga bayinsa dan tsoron azabar Allah.
  2. Sakayya daga azzalimi in ya kasance daidai da gwargwadan zalinci ko kasa daga gare shi to shi halal ne, amma kari to haramun ne.
  3. Kwadaitarwa akan kyakkyawar mu’amalantar masu hidima da raunana.