+ -

‌عن عَلِيٍّ قَالَ: إِنِّي كُنْتُ رَجُلًا إِذَا سَمِعْتُ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَدِيثًا نَفَعَنِي اللهُ مِنْهُ بِمَا شَاءَ أَنْ يَنْفَعَنِي بِهِ، وَإِذَا حَدَّثَنِي رَجُلٌ مِنْ أَصْحَابِهِ اسْتَحْلَفْتُهُ، فَإِذَا حَلَفَ لِي صَدَّقْتُهُ، وَإِنَّهُ حَدَّثَنِي ‌أَبُو بَكْرٍ، وَصَدَقَ أَبُو بَكْرٍ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«مَا مِنْ رَجُلٍ يُذْنِبُ ذَنْبًا، ثُمَّ يَقُومُ فَيَتَطَهَّرُ، ثُمَّ يُصَلِّي، ثُمَّ يَسْتَغْفِرُ اللهَ، إِلَّا غَفَرَ اللهُ لَهُ»، ثُمَّ قَرَأَ هَذِهِ الْآيَةَ: {وَالَّذِينَ إِذَا فَعَلُوا فَاحِشَةً أَوْ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ ذَكَرُوا اللهَ فَاسْتَغْفَرُوا لِذُنُوبِهِمْ} [آل عمران: 135].

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي في الكبرى وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 406]
المزيــد ...

Daga Aliyu Allah ya yarda da shi ya ce: Ni na kasance mutum ne idan na ji wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Zai anfanar da ni daga abinda Ya so daga gare shi, Ya anfanar da ni da shi, idan wani mutum daga sahabbansa ya zantar da ni zan sa shi ya rantse, idan ya rantse mini sai in gasgata shi, cewa Abubakar Allah ya yarda da shi ya zantar da ni, kuma Abubakar ya yi gaskiya, ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Babu wani mutum da zai aikata laifi, sannan ya tashi ya yi alwala, sannan ya yi sallah, sannan ya nemi gafarar Allah, sai Allah Ya gafarta masa", sannan ya karanta wannan ayar: {Sune wadanda idan sun aikata wata alfasha ko sun zalinci kansu sai su tuna Allah sai su nemi gafarar zunubansu ga (Allah)}. [Aal-Imran: 135].

[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 406]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani bawa da zai yi zunubi, sai ya kyautata alwala, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu da niyyar tuba daga zunubinsa wannan, sannan ya nemi gafar Allah, sai Allah Ya gafarta masa. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta fadinsa - Madaukakin sarki -: {Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane}. [Aal- Imran: 135].

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwadaitarwa akan sallah, sannan neman gafara bayan aikata zunubi.
  2. Yalwar gafarar Allah - Mai girma da daukaka - da karbarsa ga tuba da neman gafara.