+ -

عَنْ ‌عَائِشَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا قَالَتْ:
تَلَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ هَذِهِ الْآيَةَ: {هُوَ الَّذِي أَنْزَلَ عَلَيْكَ الْكِتَابَ مِنْهُ آيَاتٌ مُحْكَمَاتٌ هُنَّ أُمُّ الْكِتَابِ وَأُخَرُ مُتَشَابِهَاتٌ فَأَمَّا الَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمْ زَيْغٌ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ ابْتِغَاءَ الْفِتْنَةِ وَابْتِغَاءَ تَأْوِيلِهِ، وَمَا يَعْلَمُ تَأْوِيلَهُ إِلَّا اللَّهُ، وَالرَّاسِخُونَ فِي الْعِلْمِ يَقُولُونَ آمَنَّا بِهِ كُلٌّ مِنْ عِنْدِ رَبِّنَا وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّا أُولُو الْأَلْبَابِ} [آل عمران: 7]. قَالَتْ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَإِذَا رَأَيْتِ الَّذِينَ يَتَّبِعُونَ مَا تَشَابَهَ مِنْهُ فَأُولَئِكَ الَّذِينَ سَمَّى اللهُ، فَاحْذَرُوهُمْ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 4547]
المزيــد ...

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar: {Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga gareshi akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda yake kama da juna daga gareshi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne, Ba mai tinani sai ma'abota hankula} [Aal Imran: 7]. Ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambata, to ku gujesu".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 4547]

Bayani

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar:{Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga cikinsa akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda ya yi kama da juna daga gare shi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda ya san tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne Ba mai tunani sai ma'abota hankalu}. a cikin wannan ayar Allah - tsarki ya tabbatar maSa -Ya bada labari cewa Shi ne wanda Ya saukar da Alkur’ani ga AnnabinSa, wanda daga cikinsa akwai wasu ayoyi masu bayyananar nuni, hukunce-hukuncensu sanannu ne babu rikici a cikinsu, su ne asalin littafi kuma makomarsa, su ne makoma yayin sabani, daga cikinsa akwai wasu ayoyin daban masu daukar sama da ma'ana, ma'anarsu tana rikitarwa ga wasu daga mutane, ko ya zaci cewa tsakakninsu da wata ayar akwai karo, sannan Allah Ya bayyana mu'amalar mutane tare da wadannan ayoyin.
wadanda a cikin zukatansu akwai karkata daga gaskiya sai su bar bayyayanannu, su yi riko da masu kama da juna masu daukar ma'anoni sama da daya, suna neman tayar da rikici ta hakan da batar da mutane, kuma suna neman tawilinsu akan abinda ya dace da son ransu, amma matabbata a cikin ilimi to cewa su suna sanin wadannan masu kama da junan, suna dawo da shi ga bayyananne, kuma suna yin imani da shi kuma cewa shi daga gurin Allah yake - Madaukakin sarki -, ba zai yiwu ya rikitar ba ko ya yi karo da juna, saidai ba mai tunanin hakan sai mai wa'azantuwa ma'abota hankula lafiyayyu.
Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce wa Uwar Muminai A'isha - Allah Ya yarda da ita - cewa ita idan ta ga wadanda suke neman masu kama da juna to cewa su ne wadanda Allah Ya ambace su a cikin fadinSa; {Amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata} to ku gujesu kada ku karkata zuwa gare su.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayyanannu daga ayoyin Alkur’ani ; Su ne wadanda nuninsu ya bayyana kuma ma'anarsu ta bayyana.
  2. Mai kama da juna kuma: Wanda ya dauki sama da ma'ana daya kuma ya bukatu zuwa duba da fahimta.
  3. Gargadarwa daga cakuduwa da ma'abota karkata da 'yan bidi'a da wanda yake jefa mushkiloli dan batar da mutane da sa su kokwanto.
  4. A karshen ayar da fadinSa - Madaukakin sarki -: {Ba mai tunani sai ma'abota hankula} jirwaye mai kama da wanka ga karkatattu, da yabo ga matabbata a ilimi, yana nufin: Wanda bai yi tinaniba bai wa'azantuba, kuma ya bi son ransa to ba ya daga ma'abota hankula.
  5. Bin masu kamanceceniya da juna sababine ga karkatar zuciya.
  6. Wajabcin dawo da ayoyi masu kamanceceniya da juna wadanda ba'a fahimtar ma'anarsu zuwa ga ayoyi bayyanannu.
  7. Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya sanya sashin Alkur’ani bayyananne, da wani sashinsa kuma mai kama da juna; dan jarraba mutane dan kuma ma'abota imani su ware daga ma'abota bata.
  8. A cikin afkuwar mai kama da juna a cikn Alkur’ani: Bayyanar da falalar malamai akan wasunsu, da sanarwar takaituwar hankula; dan su mika wuya ga Mahaliccinsu su yi ikirari da gajiyawarsu.
  9. Falalar tabbata a cikin ilimi da wajibcin tabbata a cikinsa.
  10. A hukuncin tsayawa akan {Allah} daga fadinSa: {Kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah da matabbata a cikin ilimi} a kwai maganganu biyu na masu tafsiri:
  11. Wanda ya tsaya akan {Allah}, sai ya zama abin nufi da tawili shi ne sanin hakikanin abu da yadda yake da abinda babu wata hanya zuwa riskarsa kamar al'amarin rai da Alkiyama wadanda Allah ne Ya kebantu da saninsa, matabbata a cikin ilimi suna imani da shi suna fawwala hakikaninsa zuwa ga Allah, sai su mika wuya su kubuta.
  12. Wanda kuma ya zarce (a karatu) bai tsaya a {Allah} ba, sai abin nufi da tawili ya zama fassara da bayyanarwa, sai Allah Ya zama Ya san shi matabbata a cikin ilimi suma sun san shi , sai su yi imani da su kuma su dawo da su ga bayyananne.