+ -

عَنْ ‌عَدِيِّ بْنِ حَاتِمٍ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«الْيَهُودُ مَغْضُوبٌ عَلَيْهِمْ، وَالنَّصَارَى ضُلَّالٌ».

[صحيح] - [رواه الترمذي] - [سنن الترمذي: 2954]
المزيــد ...

Daga Adi Dan Hatim daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Yahudawa an yi fushi da su, Kiristoci kuwa batattu ne".

[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi] - [سنن الترمذي - 2954]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Yahudawa wasu mutanene da aka yi fushi da su; domin cewa su sun san gaskiya amma ba su aiki da ita. Kiristoci kuwa wasu mutanene ne batattu; domin cewa su sun yi aiki ba tare da ilimi ba.

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hadawa tsakanin ilimi da aiki da shi, tsira ne daga tafarkin wadanda aka yi fushi da su da kuma batattu.
  2. Tsoratarwa akan tafarkin Yahudawa da Kiristoci, da lazimtar hanya madaidaiciya wacce ita ce Musulunci.
  3. Kowanne daga Yahudawa da Kiristoci batattune an yi fushi da su, saidai mafi kebantar siffofin Yahudawa ita ce fushi, kuma mafi kebantar siffofin Kiristoci ita ce bata.