عَنْ قَتَادَةَ رحمه الله قال:
حَدَّثَنَا أَنَسُ بْنُ مَالِكٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَجُلًا قَالَ: يَا نَبِيَّ اللهِ كَيْفَ يُحْشَرُ الْكَافِرُ عَلَى وَجْهِهِ؟ قَالَ: «أَلَيْسَ الَّذِي أَمْشَاهُ عَلَى الرِّجْلَيْنِ فِي الدُّنْيَا قَادِرًا عَلَى أَنْ يُمْشِيَهُ عَلَى وَجْهِهِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ؟» قَالَ قَتَادَةُ: بَلَى وَعِزَّةِ رَبِّنَا.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6523]
المزيــد ...
Daga Katada - Allah Ya yi masa rahama - ya ce:
Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya zantar damu cewa wani mutum ya ce: Ya Annabin Allah ya za’a tashi kafiri akan fuskarsa? Ya ce: " Shin wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama yana da iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alkiyama ba?"Katada ya ce: Eh na rantse da buwayar Ubangijinmu.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6523]
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya za'a tashi kafiri akan fuskarsa a ranar Alkiyama ?! sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce; Shin yanzu wanda ya tafiyar da shi akan kafafuwa biyu a duniya bai zama mai iko akan ya tafiyar da shi akan fuskarsa a ranar Alkiyama ba?! Allah Mai ikone akan dukkan komai.