عَنْ ‌أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ:
قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِعَمِّهِ: «قُلْ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، أَشْهَدُ لَكَ بِهَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ»، قَالَ: لَوْلَا أَنْ تُعَيِّرَنِي قُرَيْشٌ، يَقُولُونَ: إِنَّمَا حَمَلَهُ عَلَى ذَلِكَ الْجَزَعُ لَأَقْرَرْتُ بِهَا عَيْنَكَ. فَأَنْزَلَ اللهُ: {إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ } [القصص: 56].

[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya cewa Baffansa; "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama", ya ce: Da badan Kuraishawa zasu aibatani ba, zasu ce: Razani da tsoron mutuwa ne suka kai shi haka ba da na faranta ranka da ita. Sai Allah Ya saukar: {Lallai kai ba zaka shiryar da wanda ka so ba saidai Allah Yana shiryar da wanda yake so} [Al-Kasas; 56].

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nema daga baffansa Abu Dalib alhali shi yana magagin mutuwa da ya furta; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan ya cece shi da ita ranar Alkiyama , kuma ya yi masa shaidar Musulunci, sai yaki furta shaidar dan tsoron kada Kuraishawa ta zargeshi ta ce da shi: Cewa shi ya musulunta ne saboda tsoron mutuwa da rauni! sai ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi: Da badan haka ba da na shigar da farin ciki a zuciyarka da furta shaidar, na isar da burinka har ka yarda! sai Allah Ya saukar da ayar da take nuni akan cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakar shiriya ta dacewa da Musulunci, kawai Allah - Mai girma da daukaka -Shi kadai ne Yake datar da wanda Yake so. Kuma Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -yana shiryar da halitta ta shiryarwa da bayani da kira zuwa hanya madaidaiciya.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Ba'a barin gaskiya dan tsoro daga zancen mutane.
  2. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kadai yana mallakar shiriyar nuni ne da fadakarwa kawai ba shiriyar dacewa ba.
  3. Halaccin ziyarar kafiri mara lafiya dan kiransa zuwa ga Musulunci.
  4. Kwadayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan kira zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - a kowane hali.