+ -

عن أنس -رضي الله عنه - أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: "إذا أراد الله بعبده الخير عجل له العقوبة في الدنيا، وإذا أراد بعبده الشر أمسك عنه بذنبه حتى يُوَافِيَ به يومَ القيامة".
[صحيح] - [رواه الترمذي]
المزيــد ...

Daga Anas -Allah ya yarda da shi- Manzon Allah -Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi- ya ce: "Idan Allah ya so Alkairi ga bawansa sai ya gaggauta masa Ukuba tun daga Duniya, kuma Idan ya so Sharri da Bawansa sai ya kame ga barin kamashi da laifinsa har sai yaje Ranar Lahira.
[Ingantacce ne] - [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

Bayani

Manzon Allah -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- cewa daga Alamar son Allah bawan sa da Alkairi yayi masa Magani da yi masa wata ukuba akan zunubansa a cikin Duniya har ya futa daga Duniya kuma babu komai akansa na zunubi da za'a kama shi da shi Ranar Alkiyama; domin cewa duk wanda akai masa Ukuba a Duniya ti Ukubarsa a Lahira zatayi Sauki, kuma yana daga cikin Alamomin nufin Sharri ga bawa a yi watsi da shi da Zunubansa a Duniya har yaje Ranar Al-kiyama da Tarin zunubansa har Allah ya yi masa sakamako da abunda ya cancance shi Ranar Alkiyama.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa
Manufofin Fassarorin