عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«انْظُرُوا إِلَى مَنْ أَسْفَلَ مِنْكُمْ، وَلَا تَنْظُرُوا إِلَى مَنْ هُوَ فَوْقَكُمْ، فَهُوَ أَجْدَرُ أَلَّا تَزْدَرُوا نِعْمَةَ اللهِ عَلَيْكُمْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2963]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ku yi duba zuwa ga wanda yake ƙasa da ku, kada ku yi duba zuwa ga wanda yake sama da ku, hakan zai sa (ku godewa Allah) ba za ku raina ni’imominSa gareku ba».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2963]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi ya yi duba a cikin al'amuran duniya a matsayi da dukiya da kuma alfarma da wasunsu zuwa ga wanda yake ƙasa da shi a hali, kuma kada ya yi duba a cikin al'amuran duniyarsa zuwa ga na sama da shi wanda ya fi shi, domin wannan duban zuwa ga na ƙasa shi ne mafi cancantar da zai sa ba zaka wulaƙanta ni'imar Allah gareka ba.